Manyan malamai sukan tarbiyyantar da wadanda za su gaje su. Haka lamarin yake a kowane fage na ilimi ko sana’a.
A harkar kwallon kafa ma an samu irin wadannan manyan manajoji da suka koyar da wadanda suka zo suka yi suna a bayansu.
Daga cikin manyan manajoji ko kwaca-kwacen da suka bar magada a duniyar kwallon kafa akwai Rinus Michels da Johan Cruyff, sai manajan da ke tashe a yanzu Pep Guardiola.
Akwai masu ganin cewa ba a taɓa samun koci kamar Guardiola a tarihin kwallon kafa ba, saboda yadda ya jagoranci kungiyoyi da dama a duniya kuma ya kai su ga nasara.
A kakar wasa ta bana (2024/2025) kocin mai shekara 53 zai samu kansa yana fafata gasa da kwaca-kwacen da ya horar da su harkar kwallon kafa suka dauki darasi daga gare shi yanzu kuma suke jagorantar wasu kungiyoyin kwallon kafa a sassan Turai.
Tsofaffin ’yan wasa da masu horarwa da Guadiola ya horar da suka zama manajojin da za su yi gasa da tsohon kocinsu suna da dama amma mun zaɓo fitattu biyar daga cikinsu da za su jagorancin manyan kungiyoyi a kakar bana, kamar yadda muka samo daga kafar labarai ta Football Faithful.
Mikel Arteta —Arsenal
Daga dan gaban goshi zuwa abokin gasa. Aikin koci na Mikel Arteta ya faro daga fagen koyarwa na Guadiola lokacin da yake Manchester City, inda ya shafe shekara uku yana aikin koyo daga mai gidan nasa.
Arsenal ta dauki tsohon Kyaftin dinta aikin horarwa, kuma tun lokacin tauraruwar Arteta take haskakawa, inda ya mayar da Gunners kamar yadda ake kiran Arsenal babbar mai kalubalantar mamayar da Manchester City take yi a gasar Premier.
’Yan Arewacin Landan din hakurinsu ya biya ta hanyar samun Arteta a matsayin koci.
Mikel Arteta ya lashe wasa 100 a gasar Premier daga cikin wasa 169 da ya jagoranta, wanda shi ne karo na biyar mafi sauri ga duk wani manaja.
A kakar wasan da ta gabata, Gunners ce kan gaba wajen zura kwallaye, kuma ita ce ta fi tsaron baya a rukunin, inda ta gaza lashe gasar da maki biyu kacal.
Da maki 89 kungiya kan iya lashe gasar a kakar wasa 31 ta Premier da suka gabata.
Babban kalubalen da ke gabanta a kaka mai zuwa shi ne ta yi kokari ta kawo karshen shafe shekara 20 ba ta lashe gasar ba.
Erik ten Hag — Manchester United
Bayan fara horarwa a kakar wasa daya ba tare da taɓuka abin a-zo-a-gani ba, Erik ten Hag ya karɓi horar da Ƙungiyar Bayern Munich II, a lokacin da babbar kungiyar ta Jamus take karkashin jagorancin Guardiola.
Guadiola ya jagoranci Bayern ta lashe gasar Bundesliga sau uku a jere, yayin da Ten Hag ya samu dada gogewa a horar da kwallo a kungiyar ta biyu, bisa karuwa da babban kocin.
“Yana da wahala ka ba da labari, hakika yana da wahala ka kawo haka a cikin dakika 30,” Ten Hag ya fadi a shekarar 2023 lokacin da aka tambaye shi me ya koya daga Guadiola.
“Hanya mafi dacewa? A kan nuna kwazo, ka zamo mai kwazo, ka buga kwallo.
“Babban abin da ake nema a kwallo, shi ne sakamako mai kyau, kuma ana so ka yi haka ta wata hanya, ka zamo mai kwazo, mai bayar da mamaki, mai sanya nishadi, babban abin da ake nema a kwallo shi ne samun nasara da kuma burge magoya baya, abin da aka fi a kwallo ka burge masu kallo,” in ji Ten Hag.
Ten Hag ya ci kofuna biyu a kaka biyu da ya yi da Manchester United duk da sukar da ake yi kan rashin kataɓus a gasar Premier a kakar wasa ta 2023/2024.
Lashe Kofin Ƙalubale (FA Cup) a karo na biyu, wata nasara ce da ya samu bayan doke Manchester City ta Guardiola a filin wasa na Wembley.
Xabi Alonso — Bayer Leverkusen
Xabi Alonso shi ne kocin da aka fi nema a yanzu, bayan da ya jagoranci Bayer Leverkusen ta kafa tarihi a kakar wasa ta 2023/2024.
Leverkusen ta lashe gasar kasar Jamus a karon farko a cikin shekara 120 da kafuwar kungiyar, inda ta zamo kungiya ta farko a Jamus da ta lashe gasar Bundesliga ba tare da da ta rasa wani wasa ba.
Lashe gasar DFB-Pokal ya kara wa kungiyar tagomashi, sai dai abin da ya fi faranta wa Leverkusen rai shi ne kin amsa tayin da Bayern Munich da Liverpool suka yi wa Alonso, inda ya amince ya ci gaba da zama a kungiyar.
Real Madrid ce ta fi zama wurin da Xabi inda zai koma don kara karfafa nasarar da ya samu a kakar da ta gabata wajen horarwa.
Kuma kasancewar Alonso ya samu horo a hannun Jose Mourinho, Carlo Ancelotti da kuma wanda aka fi sani, Guardiola hakan ya bayyana a salon wasan da kungiyarsa take yi.
Yadda kakar gasar Zakarun Turai ta Leverkusen za ta kasance za ta zamo wasanni masu iya burge jama’a.
Enzo Maresca — Chelsea
Enzo Maresca shi ne yaron Guardiola na bayan nan da ya karɓi horar da wata babbar kungiya.
Mai shekara 44, ya yi aiki sau biyu a lokuta daban-daban a Etihad tare da dan Spain din. Na farko da Ayarin Bunkasa Ƙwararru (EDS) kafin ya zama mataimaki a babbar kungiyar.
Bayan karɓar aiki da Leicester a bazarar bara, Maresca ya jagoranci Ƙungiyar Foxes da ta koma rukunin baya ta lashe gasar tare da sake dawowa gasar Premier.
Rawar da ya taka a gasar rukuni na biyun ne ya sa Chelsea ta nada dan kasar ta Italiya a matsayin magajin Mauricio Pochettino a filin wasa na Stamford Bridge.
Aikin da ke gaban Maresca babba ne, shi ne na farfado kungiyar ta dawo fagen lashe babbar gasar.
Vincent Kompany — Bayern Munich
Ɓincent Kompany ya zamo tauraro a Manchester City a shekara 11 da ya yi tare da kungiyar, kuma kaka uku na karshe ya yi su ne a karkashin Guardiola.
Ɗan kasar Beljiyum din ya lashe gasar Premier biyu da kofuna uku a karkashin jagorancin dan Spain din, wannan ya sa ya gusa zuwa cikin manajoji.
Kompany ya fara nuna ne da horar da wata kungiya da ba kwararriya ba a Anderlecht kafin ya jagoranci Burnley ta koma buga Gasar Premier cikin burgewa a kakar wasa ta 2022/2023.
Duk da cewa ya gaza tabbatar da kungiyar da ake yi wa kirari da Clarets a babban rukunin, salo da dabarun mai shekara 38 din sun ja hankalin Bayern Munich wada ta nada Kompany a matsayin babban kocinta a Allianz Arena.
Bayan kai-kawo wajen neman manaja, babbar kungiyar ta Bundesliga ta yi kasadar daukar Kompany, wanda take sa ran ya jagorance ta a Gasar Zakarun Turai a badi.