Mikel Arteta ya ce, Arsenal ce za ta lashe kofin Premier League na kakar bana, ba kamar yadda ake hasashen Liverpool ba.
A ranar Laraba Gunners, wadda take da tazarar maki 11 tsakaninta da Liverpool za ta fafata da Nottingham Forest a wasan mako na 27 a Premier League.
A ranar Lahadin makon da ya gabata, Liverpool ta yi nasara a kan Manchester City da 2-0 a Etihad, bayan Arsenal ta yi rashin nasara 1-0 ranar Asabar a Emirates ta hannun West Ham.
Bayan wasan na West Ham Mikel Arteta ya zargi ‘yan wasan da rashin sa ƙwazo a fafatawar, bayan Gunners shafe kaka 21 rabon ta da kofin Premier League.
Kociyan ɗan kasar Sifaniya ya kara da cewa, ‘‘Damar ɗaukar babban kofin tamaula na Ingila na bana ba a hannuna yake ba.’’
To sai dai a shirin da Arsenal ke yi na karawa da Forest a ranar Laraba, Arteta ya ce, ba zai taɓa fitar da ran lashe kofin Premier na kakar bana ba.
Arsenal wadda take sa ran ɗaukar Premier na kakar bana ta gamu da koma-baya, saboda wasu ’yan wasanta da ke jinya.
Kai Havertz da Gabriel Jesus za su ci gaba da jinya har bayan kakar bana, ana sa ran Bukayo Saka zai koma taka leda a cikin watan Maris.
Rabon da Saka ya buga wa Arsenal tamaula tun cikin Disamba, shi kuwa Gabriel Martinelli na ci gaba da jinya.
Kyaftin Odegaard ya yi jinyar da bai buga wasa 12 ba tun farkon fara wasannin bana, inda kuma aka dakatar da wasu ’yan wasan Gunners.
’Yan wasa biyar na Arsenal aka bai wa jan kati a wasa 26 a Premier League kawo yanzu.
Arsernal ta daɗe tana biye da Liverpool a teburin Premier League, wanda tuni Gunners ta kai zagaye na biyu a Champions League, amma an yi waje da ita a FA da Carabao Cup.