✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da wahala City ta yi nasara a gidan Madrid — Guardiola

Karawar farko da ƙungiyoyin suka yi a Talatar makon jiya, Madrid ce ta je har gida ta lallasa City.

Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya ce damarsu ta samun nasara kan Real Madrid ’yar kaɗan ce a yayin da a gobe Laraba ƙungiyoyin biyu za su yi karon-batta a Gasar Zakarun Turai.

Ana iya tuna cewa, a karawar farko da ƙungiyoyin suka yi a Talatar makon jiya, Madrid ce ta je har gida ta lallasa City da ci 3-2, minti huɗu kafin a tashi wasan.

To sai dai gabanin karawar ta biyu da za a yi a filin wasa na Bernabeu, a wasan neman gurbin tsallakawa zagayen ’yan 16, Guardiola ya ce damar da suke da ita kan Madrid kaɗan ce, amma za su yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun yi amfani da ita.

City dai ta farfaɗo daga dukan da ta sha a hannun Madrid a wasan da ta yi da Newcastle a gasar Firimiyar Ingila, inda ta lallasa ta da ci 4 da nema, lamarin da ya sa a ke ganin wataƙila ta iya sauya sakamakon na Madrid, sai dai Guardiola ya ce ba ya tunanin hakan ta kasance.

A karawar ta gobe dai, ya zama wajibi ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin biyu ta fice daga Gasar Zakarun Turai ba tare da kai wa zagayen ’yan 16 ba, wanda ke zama karo na farko a cikin shekaru.