Sabon kocin Barcelona, Hansi Flick, ya rattaba hannun shekara biyu a ƙungiyar ƙwallon ƙafar zuwa shekarar 2026.
Flick, ya zama kocin Barcelona ne bayan da ƙungiyar ta raba gari da Xavi Hernendez a makon da ya wuce.
- An kama ɗan bindiga, an kwato kuɗin fansa a Kaduna
- Ta gurfana a gaban kotu kan cin zarafin ’yan sanda
Shugaban ƙungiyar, Joan Laporta ne, ya dage kan ƙulla yarjejeniya da Flick, bayan alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da Xavi.
Sabon kocin ɗan asalin ƙasar Jamus ya horar da Bayern Munich da tawagar ’yan wasan Jamus, kafin daga bisani ya tafi hutun horaswa.
A baya, Flick ya taɓa lallasa Barcelona da ci 8 da 2 lokacin da yake jagorantar Bayern Munich a gasar Zakarun Turai.
Sai dai Xavi a jawabinsa na ƙarshe a matsayin kocin Barcelona, ya gargaɗi Flick cewar zai fuskanci babban ƙalubale a ƙungiyar.
Hakan dai ba zai rasa nasaba da irin halin matsin tattalin arziƙi da ƙungiyar ke ciki ba.