✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda direba ya yi ajalin daliba a wajen tarbar gwamnan Gombe

Direban ya yi awon gaba da dalibar yayi da suke tsaye a bakin titi.

Wata dalibar Sakandaren Kimiyya da ke garin Kumo a Jihar Gombe, Rahab Hassan ta rasa ranta yayin da wani direba ya banke ta a wajen tarbar gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya.

Lamarin wanda ya faru a ranar Laraba yayin ziyarar gwamnan, an samu wani direba da ke tukin ganganci da sunan murnar zuwan direban ya make ta.

An yi gaggawar garzaya wa da ita asibiti, amma kafin a karasa rai ya yi mata halinsa.

Rahab na daga cikin sauran dalibai da suka fito kan titi don tarar gwamnan da zai kai ziyarar duba aiki a garin na Kumo.

Rahab Hassan, ’yar asalin garin Tula Baule, mai shekara 17 da haihuwa da ke aji daya na babbar sakandare wato (SS1), mai motar ya gagara shawo kan motar ne ya bugeta a bakin makarantar da su ke jere don jiran isowar gwamnan.

Da ya ke zantawa da manema labarai, mahaifin Rahab Hassan, Hassan Sunkutale, ya bayyana takaicinsa kan faruwar lamarin.

Rahab Hassan, dalibar da ta gamu da ajalinta a wajen tarbar gwamnan Gombe
Rahab Hassan, dalibar da ta gamu da ajalinta a wajen tarbar gwamnan Gombe

Ya ce ‘yarsa da ya ke yi wa hidima don ganin ta samu ilimi kuma yake fatan nan gaba za ta taimake shi a rayuwa sai gashi a kan tarar gwamna ya rasa ta.

Mahaifin ya koka kan cewa ya tura ‘yarsa makaranta, don haka bai ga dalilin fito masa da ita bakin titi tarbar dan siyasa ba.

Shi ma kanin mahaifin Rahab, Musa sunkutale, cewa ya yi su makaranta su ka kai ‘yarsu don ta yi karatu.

Sai dai sun bukaci a musu adalci tare da bi musu kadin kisan ‘yarsu.

Kazalika, sun koka kan cewar tun bayan faruwar lamarin babu wani jami’in gwamnati da ya kai musu ziyara da sunan gaisuwa ko ta’aziyya.

Don haka sun bukaci gwamnatin jihar ta biya su diyyar kisan ‘yarsu da aka yi.

Mun yi kokarin jin ta bakin Kwamishinan Ilimi na Jihar Gombe Mista Dauda Batari Zambuk, amma hakar ba ta cim ma ruwa ba, inda ya ce ba shi da ta cewa kan lamarin.