Wani yaro dan shekara 11, Humphreys Chipeta, ya mutu bayan shan kwalba biyar ta giyar Kachasu a gasar shan barasa da aka yi a Mzimba, wani gari a kasar Malawi.
Yaron wanda a cewar abokanansa, ya zuwa lokacin gogaggen mashayi ne wanda ya fadi ba rai yayin da ake zagayen karshe na gasar.
Cikin rahoton da jaridar Vanguard ta wallafa, an sanya kwacha dubu 20 a matsayin kyautar lashe gasar ta yara ‘yan kasa da shekara 14 wadanda suka goge wajen shan barasa.
Wani ganau da ya ba da shaida, Emmanuel Chirwa, ya ce “gasar mataki-mataki ce. Sun yi amfani da shekaru kamar yadda ake yi a kwallon kafa; akwai ta ‘yan kasa da shekara 14 da kuma ‘yan kasa da shekara 21, sannan sai kuma ta manya.”
Ya kara da cewa: “Yawanci irin haka tana faruwa kuma yaron ya mutu ne a yana kokarin kare kambun nasarar lashe gasar da aka yi ta karshe.”
“Amma muna tsammanin akwai makarkashiya a lamarin da ya janyo mutuwarsa. Domin idan ba haka, yaron ba farin shiga bane, kwararren mashayi ne.”
A cewar Chirwa, daga cikin ka’idodin shiga gasar, dole ne sai mutum ya ba da Kwacha 1000 sannan ya cika cikinsa da abinci kafin a fara gasar.”
“Saboda haka bai mutu ba a sakamakon rashin cin abinci gabanin fara gasar. Duk sun ci abinci, amma akwai dai abin da ya faru,” inji Chirwa.
Haramtacciyar gasar da aka gudanar a yankin Chimbongondo da ke karkashin masarautar gargajiya ta Kampingo Sibande a garin Mzimba, ta sake bankado yadda kananan kara ke ci gaba da shan barasa a fadin kasar.
Wani jami’in kare hakkin yara a yankin, Shanks Nkhata, ya sha alwashin zai bi diddigi a kan lamarin domin tabbatar da an haramta shan barasa a yankin.
“Mun samu labarin yaron dan aji bakwai ne a Firamaren Kafulufulu inda bayan an shiga hutun annobar Coronavirus ya zama kwararren mashayi.”
“Shi kadai na sani a yanzu, amma akwai su da dama kuma zan bincika domin a kawo karshen mummunar dabi’ar,” inji Nkhata.