A ranar Asabar, 18 ga watan Yuli al’ummar garin Yammama da ke Karamar Hukumar Malumfashi ta jihar Katsina suka wayi gari da wani abin alhini na mutuwar yara bakwai ‘ya’yan mutum daya.
Yaran sun gamu da ajalinsu ne yayin da suka je gona yin ciyawa, inda suka ci karo da bom na gurneti, cikin rashin sanin illarsa suka dauka suka nufi gida da shi.
Yadda gurnetin ya fashe a hannun yaran
Wani shaida ya ce yaran na dauke gurnetin a lokacin da ya fashe, kuma kararsa ta jefa al’ummar garin cikin firgici, wadanda daga bisani suka taru a wajen domin gane wa idanunsu abin da ya faru.
Ya ce wata mace ta ci karo da yaran a lokacin da suke tafe da gurnetin, ta kuma umarce su da su jefar da shi.
“Yaran sun jefar da gurnetin a lokacin da matar ta umarce su da yin haka, sai dai sun koma sun sake dauka, da suka ji diyar matar tana cewa za ta je ta dauka ta sayar wa ‘yan gwangwan a cikin gari.
“Maganar da yayrinyar ta yi ne ya bai wa yaran kwarin gwiwa suka sake daukar gurnetin.
“Juyawar matar da diyar tata ke da wuya sai suka ji karar fashewar wani abu, ko da suka juya sai suka tarar da gawarwakin yaran a warwatse, tare da wasu da suka sami munanan raunuka”, inji shi.
Ya kara da cewa yaran sun cire kunamar jikin gurnetin, wacce ke hana shi tashi, lamarin da ya sa shi fashewa a hannunsu.
Gurnetin ya fashe ne a daidai gonar kaji da take wajen garin Yammama, inda yara shida suka rasu nan take, yayin da na bakwai ya rasu a asibiti, wasu biyar kuma suka jikkata.
An yi wa yaran sutura
Wakilin Aminiya ya halarci sallar jana’izar yaran shida wadda Danejin Katsina, Hakimin Mahuta, Alhaji Bello Abdurkadir Yammama ya jagoranta.
Sallar jana’izar ta samu halarcin tarin mutane da suka cika da alhini ciki harda Hakimin Malumfashi, Mai Shari’a Sadik Abdullahi Mahuta (Murabus).
Mahaifin yaran Malam Iliya Adamu Yammama ya kadu matuka yayin da aka binne shida daga cikin ‘yayansa ake kuma dakon gawar na bakwai da za a kawo ta daga asibiti.
Wakilin Aminiya ya gane wa idanunsa yara hudu da suka jikkata suke kuma samun kulawa a asibiti.
Kakar wasu daga cikin yaran ta bayyana sunayen su kamar haka, Fatima Iliya, da Iliya Iliya, sai Rabi Lawal, da Maryam Danmalam.
Ana tababar asalin gurnetin
Wasu mazauna yankin na zargin gurnetin ka iya kasancewa na jami’an tsaro ne da ke aikin ba da tsaro a yankin ko kuma ta ‘yan bindiga ce da ke addabar sassan jihar.
Sai dai kuma yankin da lamarin ya faru ba a taba samun matsalar ‘yan bindigar ba.
Gurnetin sojoji ce, inji ‘yan sanda
‘Yan sanda a jihar Katsina sun yi wa matar farko da ta shaida faruwar lamarin tare da diyarta tambayoyi.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan, SP Gambo Isa ya ce binciken da suka yi a karon farko ya gano cewa gurnetin na Rundunar Sojin Najeriya ne.
Gwamnatin Jihar Katsina ta ce mutum takwas ne suka rasu sakamakon fashewar gurnetin.