✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Boko Haram ta yi wa mutum 11 yankan rago a Geidam

Mayakan kungiyar kutsa cikin garin suna wa mazauna kisan gilla a cikin dare

Mayakan Boko Haram sun yi wa mutum 11 yankan rago a wani sabon harin da suka kai a Karamar Hukumar Geidam ta  Jihar Yobe.

Maharan sun ajiye baburansu ne sannan suka shiga garin a kafa suka yi aika-aikar a ranar Laraba, a garin Geidam, mahaifar Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali-Baba.

Wasu rahotanni na cewa adadin mutanen da kungiyar ta ISWAP ta yi wa yankan rago sun kai 11, sai dai kawo yanzu hukumomi ba su yi magana kan lamarin ba.

Wakilinmu ya gano cewa tun farko sai da maharan suka shiga Makarantar Sakandaren Kimiyya da Fasaha ta Gwamnati da ke Geidam suka kona ajujuwa biyu suka yi wa wani mutum yankan rago a gidajen ma’aikatan makarantar.

Daga nan suka wuce zuwa wata mashaya suka yi wa akalla mutum tara yankan rago kafin suka sulale ba tare da jami’an tsaro sun ji duriyarsu ba.

A safiyar Alhamis din nan Aminiya ta kawo rahoto cewa mutanen garin Geidam sun kwana ba su runtsa ba saboda karar fashewar abubuwa a cikin dare.

Yadda abin ya faru

Aminiya ta gano cewa ’yan ta’addar sun yi yunkurin shiga garin na Geidam ne tun kusan magariba,  a ranar Laraba amma sojoji da ke garin suka fatattake su.

Daga baya cikin dare wajen karfe 11 suka sulalo zuwa cikin garin ta unguwar Marawa a kusa da Makarantar Sakandaren Kimiyya, inda yanka mutum guda.

Daga nan suka wuce zuwa Unguwar Kwari suka yanka wasu mutum takwas ciki har da wata mace.

Wani magidanci a Unguwar Kwari ya shaida wa Aminiya ta waya cewa ’yan ta’addar sun shiga garin ne da misalin karfe 11.00 na dare, suka nufi wani wata mashaya a unguwar, inda suka yi wa mutum takwas yankan rago tare da raunata wasu biyu.

Sun shammace mu

Mazauna yankin sun kara bayyana cewa maharan sun shammace su da kuma sojojin  da ke Geidam ba saboda ba a yi artabu ba.

A cewarsu, sun yi aiwatar da wannan aika-aika ne cikin sirri sannan suka fice suka tsere.

Ko da yake sojoji da samun labarin sun mayar da martani cikin gaggawa suka bi sawunsu, amma majiyarmu ta ce maharan tuni suka tsere zuwa cikin daji ba tare da sojojin sun cin  musu ba.

Har zuwa lokacin kammala wannan wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su tabbatar da harin ko cewa wani abu kan wannan hari ba sai dai nan gaba.

Garin na Geidam ne mahaifar Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali-Baba.

Garin na da tazarar kilomita 177 daga Damaturu babban birnin Jihar Yobe, kuma yana iyaka da Jamhuriyar Nijar da Damasak, daya ne daga cikin tungar ’yan ta’adda a jihohi Yobe da Borno.