Kwaskwarima da sauye-sauyen zamani da gyaran hanyoyi da birnin Kano ya samu a baya-bayan nan, musamman zamanin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso sun kawo raguwar cinkoson ababen hawa a kan tituna. Wakilinmu wanda ya ziyarci birnin kwanakin baya, ya ruwaito cewa duk wanda ya kwana biyu bai je Kano ba sai ya yi tambaya kafin ya kai inda ya nufa saboda sauyawar birnin:
A shekaru baya, Kanawa na shan takala daga abokan wasansu Zage-zage, inda suke cewa sai Kanawan sun zo Zariya suke hawa gadar-sama sannan su koma Kano su ba da labari.
To amma yanzu birnin Kano ya samu gadojin gadojin sama fiye da Zariya, kai tuntuBe gushin tafiya har ma yana da gadar-Kasa, duk sakamakon juyin juya-halin jar ta tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso.
Bugu da Kari, kana iya kewayawa a sassan birnin Kano a yanzu, ba tare da ka sha fama da mugun cinkoson abubuwan hawa da birnin ya yi suna da shi a baya ba. Domin a yanzu cinkoson ya zama tarihi saboda an samar da Karin tituna da tagwayen hanyoyi wadanda mai tafiya a kan abubuwan hawa babu ruwansa da jira a mahada mai aiki da fitilar bayar da hannu, wucewa kawai zai yi, wadanda za su miKe su ne fitilar za ta tsayar da su. Amma na lura saboda halin ’yan bana-bakwai na Kin bin doka da gudun wuce Kima, ya sa har yanzu jami’an tsaro suna tsayuwa a wadannan wurare don maganin masu taurin kai.
Wata kwalliyar da aka yi wa birnin Kano, ita ce ta matasa wadanda aka janye su daga shiga aikin assha irin na ’yan-daba aka samar musu da aiki da Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano da ake kira a taKaice da KAROTA. Matasan suna taimakwa wajen hana karya dokar tuKi kamar hana bin hannun da ba na mai tuKi ba da cusa mutanen da suka wuce Kima a cikin mota ko dora mata kayan da ya saBa wa doka da kuma uwa-uba hana dabbobi gararamba a kan titunan birnin.
A baya da wuya ka je Kano ba ka ga gungun dabbobi da suka hada da jakuna da tumaki da awaki suna gararamba suna neman abinci. Galibinsu cikin dauda saboda rashin kula, in ka ga an kula da su an yi musu wanka, to za a kai kasuwa ne don sayarwa, saboda su yi daraja.
A yanzu duk mai shiga birnin Kano idan ya lura zai ga cewa tun daga farkon shigarsa birnin daga ’Yan Lemo zuwa Gidan Zoo, zuwa Titin Neja, daga nan har zuwa cikin gari ta Gwauron Dutse da dan Agundi da Kumbotso, kuma a karkata zuwa unguwar Turawa (GRA) zai yi wuya ka ga jaki, ko akuya ko tunkiya balle kaza ko agwagwa. Wato da gefen gari da cikin birni da kuma Bangaren masu hannu-da-shuni doka ta mamaye su domin doka ta ja-layi cewa duk wanda ya bar dabbarsa tana watangaririya za a kama a ci tararsa.
Wannan ci gaban da aka samu a birnin Kano ya kawo sauKin zirga-zirga ga kowa domin ya kawar da daukar dogon lokaci a cikin runtsin jerin gwanon ababen hawa, wanda ya zama tarihi tare da rage hadurra sosai. Misali yadda manyan motoci da ke yawo da man fetir da manyan motocin daukar kaya da tifofi wadanda ba cika kasancewa da isassun birki ba suke jefa rayukan jama’ar birnin cikin hadari duk yanzu an samu raguwar hakan.
Sake fasalin birnin Kano ya taimaka hatta a Bangaren kiwon lafiya sakamakon raguwar hadurra. Sananne ne cewa idan aka samu hadari, akan dauki marar lafiya ne a takure cikin a-kori-kura ko KEKE-NAPEP (da ake ce wa A Daidaita Sahu a Kano ko Agwagwa-da-buje a Sakkwato) saboda Karancin motocin daukar marasa lafiya. Sannan idan aka samu aukuwar hadarin da an je ta asibiti sai an kashe dimbin kudi kafin a ba majinyaci gadon jinya. Wani hadarin kan sanya a nemi jini komai baKin talaucin dangin mutumin da ya yi hadarin. Don haka wannan inganta tituna ta rage wannan cinkoso na ba gaira-ba-sabar, tare da rage aukuwar hadurra.
Wannan aiki na sake fasalin birnin Kano ya zo ne a daidai lokacin da mutanen wannan Bangare na Arewa ba su cika son ci gaba ba, domin suna ganin ba za su yi iya barin gidajensu nag ado ko unguwanninsu ko wani abu nasu ba, domin a gudanar da wani aiki na ci gaban al’umma ba. Wannan ya sa yawancin garuruwan Arewa idan aka ce za a fadada hanyoyi sai an biya maKudan kudi kafin su bari a rusa musu gidajensu na gado.
Ya kamata gwamnatocin jihohin Arewa su kwaikwayi yadda gwamnatin Jihar Kano ta yunKura wajen sake fasalin birnin Kano domin sake fasalin nasu biranen ta yadda za su rage cinkoson ababen hawa da rage aukuwar hadarurruka da ambaliyar ruwa.
Ni dai da na je birnin Kano sai da na yi tambaya tun a Kundila maganin Kauyanci don kada in Kona man fetur a banza, saboda masu iya magana sun ce da asara gara gidadanci.