Zakaran Damben Boksin na Duniya, Anthony Joshua wanda dan asalin Najeriya ya ba marada kunya a ranar Asabar da dare a kasar Saudiyya lokacin da ya doke abokin karawarsa Andy Ruiz Jr.
Zakaran kafin ya shiga harkar damben boksin ya taba zama birkila a baya.
A ranar 1 ga Yulin bana ne a wani wasa da ya ba duniya mamaki Andy Ruiz ya lallasa Joshua a birnin New York a turmi na bakwai. Sai dai Joshua ya sake sabon shiri inda a wannan karo ya casa abokin karawar tasa dan asalin kasar Meziko kuma dan kasar Amurka a halin yanzu.
Joshua a halin yanzu ya karbe kambunan Zakaran Duniya na WBA (Super), IBF, WBO da IBO ajin masu nauyi bayan da ya doke Andy Ruiz Jr.
Ga wasu bayanai game da Anthony Joshua da za su ba ka mamaki.
1. Ya taba yin aikin birkila a wani babban kamfanin gine-gine da ke kasar Ingila kafin daga baya ya shiga sana’ar dambe boksin.
2. Anthony Joshua ya taba yin fusrsuna a shekarar 2009, kan laifin da ya kira “fada kan wani abu marar muhimmanci,” inda aka makala masa wata na’ura a idanuwan kafafunsa.
3. Haka Joshua ya kusa barin dambe lokacin da aka kama shi kan mallakar tabar wiwi, amma sai ya ci sa’a aka yanke masa hukuncin yin aiki ga al’umma na tsawo wata 12 kafin a sallame shi.
4. Anthony Joshua ya fito ne daga gidan da ya daidaita. Mahaifansa, Robert da mahaifiyarsa Yeta Joshua sun rabu tun yana dan sekara 12.
5. Joshua ya taso ne a Najeriya inda ya yi makarantar kwana ta Mayflower da ke Ikenne a Jihar Ogun.
6. A makarantar ya shahara wajen kwallon kafa da wasannin gudu, har ma ya taba zama zakara inda ya lashe gasar gudu ta mita 100 acikin dakika 11.6
7. Sau daya tal aka taba kayar da Anthony Joshua tunda ya fara sana’ar damben boksin.
8. Anthony Joshua ya samu Fam miliyan 45 wanda ake sa ran yanzu za su rubanya saboda nasarar da ya samu a kan Andy Ruiz Jr a kasar Saudiyya.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yaba wa Zakaran Damben Boksin din na Duniya, Anthony Joshua, bisa nasarar da ya samu kan Andy Ruiz ranar Asabar.
Mahaifiyar Anthony Joshua, Yeta da mahaifinsa Robert Joshua ’yan asalin Najeriya ne duk da cewa an haife shi ne a Watford ta kasar Ingila.
“Na jinjina wa Zakaran Boksin Anthony Joshua bisa nasarar da ya samu a daren Asabar kan Andy Ruiz Jnr,” Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter.
“Ka saka farin ciki a zukatan miliyoyin ’yan Najeriya a gida da waje. Muna matukar alfahari da kai yanzu da kuma nan gaba,” inji Shugaban.
Anthony Joshua ya kwato kambunansa na IBF da WBA da WBO da Ruiz ya kwace daga hannunsa wata shida da suka gabata a New York.
An yi damben ne a Diriyah Arena a birnin Riyad na Saudiyya a gaban ’yan kallo sama da 14,000.
Yanzu Joshua mai shekara 30, ya shiga tarihin ’yan damben boksin na duniya da suka sake kwato kambin damben duniya ajin masu nauyi, wadanda da suka hada da Muhammad Ali da Lennod Lewis da Ebander Holyfield da Mike Tyson da Floyd Patterson.