✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda beraye suka tilasta wa manoma kwana a gonakinsu a Kano

A cikin rami dyaya sai ka same beraye sun kai sama da 20 ko 30 kamar ruwansu aka yi a gonakin.

Manoma a kananan hukumomn Kura da Garun Malam da Bunkure a Jihar Kano sun koka kan yadda wasu murguza murguzan Beraye suka tilasta musu kwana a gonakinsu domin yin gadi sakamakon barnata musu amfanin gona.

A cewarsu, duk da cewar babu irin nau’in kayan amfani gona da wadannan beraye ba su lalatawa, amma sun fi lalata Masara.

Sun kuma bayyana cewa, berayen sun zame musu annoba, musamman ganin cewa duk irin maganin da aka saka musu ba ya kashe su.

Ganin cewa berayen ba su cin duk wani magani da aka sanya musu hakan ta sa manoman suka dauki matakin yin fito-na-fito da su, kamar yadda wani manomi ya shaida wa Aminiya.

Manomin ya bayyana cewa, beraye sun fi son hasken fitila, lamarin da ya sanya manoman suke kunna musu fitila da dare idan sun fito sai samu su kashe su.

Sannan sun kuma ce, an ɗauki tsawon lokaci berayen suna uzzira musu kuma suna zuwa ne lokacin sanyi.

Malam Ado Abdullahi manomi a garin Barkum ya shaida wa Aminiya cewa, girman berayen sun kai kamar girman karamar gafiya.

“Wannan annoba ce kai tsaye domin kowa ya ce bai taba ganin irin wadannan berayen ba.

“Hatta kulawa masu kama beraye ba su kama su domin sun ce ba su son su.”

Malam Ado ya kuma ce, da zarar amfani ya fara fitowa berayen sukan hau su guntule samansa sai kuma su hake kasan su cinye kwayar.

Sannan ya ce, “Ba wai amfanin da ya fara fitowa suke yi wa illa kadai ba, har wanda ba a dade da shukawa ba sukan tone shi su cinye.”

Shi kuwa Najib Aliyu Karfi cewa ya yi, manoman sun rasa yadda za su yi da berayen domin ana kashe su, amma kara yawa suke yi.

Ya ce a cikin rami daya sai ka same beraye sun kai sama da 20 ko 30 kamar ruwansu aka yi a gonakin saboda yawa.

Ya kuma ce a yanzu manoma fita suke da daddare, inda suke faraurtarsu don kashe su ta hanyar haka rami a kone su a ciki.

“Da yawa daga cikinmu idan dare ya yi hana idonmu barci muke yi, sai mu ɗauki fitilu mu zo gonar don ganin cewa berayen ba su lalata mana amfani ba.

“Sannan a gefe guda kuma kasancewar berayen sun fi son hasken fitila sai ka ga sun fito, mu kuma sai mu yi amfani da wannan dama mu kashe wanda za mu iya kashewa domin ba su mutuwa cikin sauki,” in ji shi.

Manoman dai sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta kawo musu dauki duba da yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa, inda manoma suka kashe kuɗi da yawa wajen yin shuka ga kuma wannan annoba ta beraye da ta saukar musu, matsin zai yi yawa.

Malam Bashir Barau Malami ne a Makarantar Koyar da Dabarun Aikin Gona ta Gwamnatin Tarayya da ke Hotoro ya ce, irin wadannan beraye babu wani amfanin gona da ba su iya yi wa illa ba.

Sai dai ya yi kira ga manoma da su guji cin duk wani abu da suka sawa baki.

Baya ga illar da suke yi wa kayan amfanin gona, wadannan beraye suna kuma hawa kan karan masara su gwaigwaya.

Idan kuma shinkafa ce suna yawo a ciki wanda har su samu su kayar da ita.

Idan tumatir ne koyalo shi ma haka beran yake hawa kansa ya lalata.

Idan kuma amfanin gonar a hade yake a wuri guda, berayen sukan yi fitsari ko kashi a ciki wanda idan mutum ya shaki warin yakan iya janyo masa cututtuka.

Malamin ya kuma bayyana dalilin da ya sa ake samun beraye masu yawa a bangaren Kura da Garun Malam shi ne, saboda wadatar abinci da ruwa a yankin wanda hakan ya nuna suna koshi sosai don haka dole su hayayyafa.

Sai ya shawarci manoma da cewa duk wurin da suka san ramin bera ne su yi kokarin toshe shi don a rage yawansu.

“Haka kuma duk wurin da aka san akwai duhu to a samar da haske a wurin domin bera yana son duhu saboda a nan yake iya boyewa.

“Idan gidanka kusa da daji ne to ya kamata ka gyara shi tare da sa masa haske.

“Sannan ya kamata manoman su yi amfani da tarko don kama su,” inji shi.

Ya kara da cewa, idan har aka kashe bera to ya kamata a haka rami a binne shi ko kuma a kone shi ya zama toka don gudun yaduwar cutuka a tsakanin jama’a domin duk abin da bera ya taba zai iya kawo cututtuka.