✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Atiku ya zabi Okowa a matsayin mataimaki

Nan take Wike ya bar wurin taron bayan shugabannin PDP sun yi ittifakin Okowa ya zama mataimakin Atiku

Yunkurin karshe na masu fada a ji a jam’iyyar PDP ya kai Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa ga zama mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.

Kusoshin jam’iyyar sun yi ittifakin cewa Okowa ya zama mataimakin Atiku ne a wani dogon zama da suka yi har zuwa safiyar Alhamis a Abuja.

Daukar Okowa ya rusa yunkurin Gwamnan Jihar Ribas, Barista Nyesom Wike na zame wa Atiku Abubakar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Uwar Jam’iyyar PDP ta kira zaman ne bayan kwamitin da ta kafa domin zabo mutumin da ya fi dacewa Atiku ya dauka a matsayin mataimaki, karkashin jagorancin Manjo-Janar Aliyu Gusau mai murabus, ya mika mata rahotonsa.

Kwamitin na Aliyu Gusau ya gabatar wa jam’iyyar sunayen mutum uku da suka hada da Wike da Okowa da kuma Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel.

Majiyarmu ta ce taron da aka amince da zabin Okowa ya samu halarcin manyan shugabannin PDP, ciki har da shugabanta na Kasa, Iyorchia Ayu da Atiku da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark da Wike da Okowa da Udom Emmanuel.

Taron ya kuma samu goyon bayan sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Tun ranar Talata Aminiya ta kawo rahoto na musamman cewa Atiku ya fi son daukar Okowa a matsayin mataimakinsa, amma duk da haka ya bukaci shugabannin jam’iyyar su ba shi shawara kan mutumin da ya fi dacewa.

Wani daga cikin shugabannin jam’iyyar da ya halarci zaman na ranar Alhamis ya shaida wa wakilinmu cewa sun yi ittifakin cewa Okowa ne ya fi dacewa Atiku ya dauka a matsayin mataimaki, saboda Wike “zai yi wuyar tallatawa musamman a yankin Arewa saboda matsayinsa game da wasu batutuwa da suka shafi kasa.”

Wike ya fice daga wurin taro

Da aka tambaye shi game da martanin Wike bayan Atiku ya zabi Okowa, sai jigon na PDP ya ce, ai Wike “nan take ya wuce, amma ina tabbatar maka cewa babu inda zai je; zai tsaya mu yi aiki tare domin abin da ya faru mu zai amfana gaba daya.”

Hakazalika, babban mai goyon bayan Wike, Gwamna Ifeanyi Ugwanyi na Jihar Enugu da sauran ’yan bangarensu ba su halarci taron gabatar da Okowa ga shugabannin jam’iyyar ba a matsayin mataimaki ga Atiku ba.

Amma wani mamban Kwamitin Amintattun PDP ya ce shugabannin jam’iyyar sun lallashi Wike cewa kada ya fice daga jam’iyyar kuma za su ci gaba da magana da shi domin amfanin jam’iyyar.

Aminiya ta gano cewa baya ga taron shugabannin jam’iyyar da ya zabi Okowa iyayen Jam’iyyar PDP ba su goyon bayan Wike.

“Iyayen jam’iyyar suna da shakku a kansa saboda irin dabi’unsa; suna ganin jam’iyyar na bukatar dan takara mai saukin kai da biyayya wanda zai rika daukar umarni daga shugaban kasa idan suka ci zabe a 2023,” a cewar majiyar.

Ta kara da cewa wani abin da ya kara taimaka wa Okowa shi ne ya fito kai da fata ya taimaka wajen ganin Atiku ya kai ga nasara a zaben fitar da dan takara.

Wani na hannun daman Atiku ya ce Okowa, “Ya fitar da kudade sannan ya rika bin daliget yana neman su zabi Atiku; a 2019 ma haka ya yi wa Atiku, lokacin da shi Wike ke goyon bayan Tambuwal.”

Dalilin da na zabi Okowa —Atiku

Da yake jawabi a taron gabatar da Okowa, Atiku ya bayyana cewa duba da mawuyacin halin da Najeriya ke ciki, yana bukatar mataimaki wanda ke da gogewa ya kuma fahimci yanayin Najeriya da tattalin arzikinta da kuma halin da ’yan Najeriya ke ciki kuma zai iya kawo hanyoyin samar da ayyukan yi ga matasa da kuma karuwar arziki da wadata.

Bugu da kari, mataimakin da yake bukata shi ne mutumin da ba ya jin tsoron bayyana ra’ayinsa tare da tsage gaskiya komai dacinta a ko’ina, wanda kuma ke da nagartar da zai iya rike kujerar shugaban kasa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ya bayyana cewa wadannan su ne abubuwan da ya bayyana wa shugabannin jam’iyyar a yayin da yake tattaunawa da su don neman shawarwarinsu game da wanda zai zama abokin takararsa.

A cewar Atiku, zabar Okowa zai kara wa takararsa armashi “da kuma daidaito idan muka kafa gwamnati a 2023.”