✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

 Yadda annobar COVID-19 ta shafi bukukuwan aure

A Najeriya an samu mutum na farko da ya kamu da coronavirus ne a watan Fabrairun bana. Tun lokacin dai yawan wadanda aka tabbatar sun…

A Najeriya an samu mutum na farko da ya kamu da coronavirus ne a watan Fabrairun bana.

Tun lokacin dai yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar yake ta karuwa.

A kokarinsa na dakile yaduwar annobar, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin garkame Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Ogun da Lagos, in ban da ayyukan da suka zama lallai da tilas.

Rufe masana’antu da ma sauran harkakokin tattalin arziki ya shafi dukkanin sha’ani a duniya baki daya.

Ma’aurata sun kosa

Wani sha’anin rayuwa da lamarin ya yi wa illar gaske shi ne harkar shirya bukukuwan aure wadda ke lakume miliyoyin naira.

Kafin bullar cutar, hidimomin aure da dama na gudana yadda ya kamata har sai da gwamnati ta bayar da umurnin zaman kulle.

Ma’aurata da masu wasu sana’o’i, musamman ma masu sayar da abinci da masu dab’i da masu daukar hoto da kuma masu sana’ar kade-kade a wajen bukukuwa sun bayyana wa Aminiya yadda lamarin ya shafe su.

A watan Disamban 2019 Kalim ya fara neman Zaynab – saura wata kadan Zaynab din ta zama amaryarsa.

Bisa al’ada a kan fara hidimomin aure gabanin ranar bikin – inda ko wanne iyali suke kokarin dafa wa ‘ya’yansu don ganin nasarar wannan muhimmiyar rana a rayuwarsu.

An tsara yin bukin ranar 21 ga watan Maris; sai dai shirin ya wargaje.

“Ina cike da shaukin ganin na zama magidanci, shirye-shiryen ganin wannan ranar sun kasance abin tunawa matuka, don haka ba zan ce zaman kullen ya wargaza mini fatana ko mafarkina ba.

“Kawai dai an dage bukin ne zuwa wani lokacin”, inji Kalim.

Amarya ma ta zaku

Ita ma amaryar ta zaku a kawo karshen zaman kullen wala’alla ta shaida muhimmiyar ranar da take ta muradi.

“Na yi shiri sosai game da wannan muhimmiyar ranar a rayuwata, ina son masoyana da aminai da kuma iyalina duk su hallara domin taya ni murna.

“Ina son bukin ya kasance abin tunawa a tsawon rayuwa domin haka ne ni da mijin da zan aura muka yanke shawarar jira har lokacin da lamura za su daidaita,” inji Zaynab, amaryar da Kalim zai angwance da ita.

A daidai ganiyar dokar hana tara mutane fiye da 50 a waje guda, shi kuwa wani mai suna Johnson ya yi katarin auren masoyiyarsa mai suna Esther Abayomi a ranar 21 ga watan Maris.

“Da ma can mun riga mun kammala shirye-shiryenmu don haka ba za mu dakatar da bukin ba, lallai mun daura auren, amma mun kashe makudan kudi,” inji Johnson.

Ba abinci, ba bukin aure

Abinci dai wani muhimmin abu ne a sha’anin aure wanda ba za a yi wasa da shi ba.

Wata mai sana’ar dafa abincin sayarwa a birnin Badun, Faith Imosemi, ta ce garkamewar ta dama mata lissafi.

“Kusan dukkanin jingar da aka ba ni gabanin garkamewar, yanzu an fasa, wasu sun soke odarsu ciki har da ta kek din tuna ranar haihuwa da kuma dabgen bukin aure.

“Hakan ya faru ne saboda kowa yana cikin zullumi da tsoro.

“Ganin cewa da ma na riga na tanadi kayayyakin hade-haden girkin, amma ba zan iya cinye shi ni kadai ba a gida, don haka ina fatan ba za su lalace ba, saboda asara za ta mini yawa.

“Sai dai har yanzun nan, da akwai wadanda suke odar kek, amma dai abinci kam babu mai nuna sha’awarsa a kai saboda yadda kowa ke cikin fargaba, hatta wuraren cin abincin ma lamarin bai bar su ba.

“Kai lamarin ma ya wuce soke bukukuwan aure, gaskiyar abin da ke faruwa game da wannan annobar shi ne ta zama tamkar wutar daji ga ko wacce harkar cinikayya”, inji ta.

Harkar dab’i ta shiga tasku

Ita ma harkar dab’i ta shiga tasku sakamakon lamarin, dukkan ayyukan da aka karba daga kwastomomi gabanin zaman kullen yanzu an dakatar da su – ta yadda masu bukatar ayyukan suka gaza biyan kudin abin da suke da muradi.

Sannan kuma an dakatar da batun wallafa kayayyakin tukwici da ake rabawa lokacin aure da aka bayar da odar yin su kafin aure.

“A gaskiya hakan ya yi matukar tasiri a kan sana’armu domin muna ci gaba da rike kayayyakin jingar da muka amsa. Kuma ba mu iya mayar da su ga wadanda suka sayar mana tun farko,” inji Ahmed Abdullahi, wanda ke harkar dab’i a Ilori.

“Corona ta shafi dukkanin harkokin tattalin arziki, kowa na ta fadi-tashin ganin ya samu na kaiwa bakin salati.

“Idan dai babu bukukuwa, to ai babu bukatar mai’aikatan da za su yi wa baki zagi a yayin taruka.

“Don haka yanzu ina zaman gida ne kuma bana aikin komi”, inji Aishah Abdulsalam, wata mai tarbar baki a wurin bukukuwa da ke zaune a Legas.

Ita ma sana’ar kade-kade, jigo ce a lokacin bukukuwa.

Kayan kida sun yi kura

Lokacin da Aminiya ta ziyarci shagon wani makadi mai suna Gospel Music Band, ta tarar da kayan kidan duk sun yi kura – ga alama ya dauki lokaci mai tsawo bai yi aiki da su ba.

“Na rasa wasu manyan bukukuwan har guda biyar, duk a sakamakon dokar zaman kullen da kuma umurnin a ba da tazara da juna.

“Wasu daga cikin masu bukukuwan sun riga sun ma biya, amma ana sanar da kafa dokar kullen sai suka nemi na dawo musu da kudinsu, don haka yanzu ba ni da ko ranyo,” inji wani DJ a Abuja.

Ajiya, masu iya Magana suka ce, maganin wata rana; ajiyar wani abu da za a gani a rika tuna abin da ya faru tabbas muhimmin lamari ne, kuma hanya daya da za a cimma hakan ita ce daukar hotuna.

Daukar hoto ba labari

Wani mai sana’ar daukar hoton a Abuja, Emmanuel Chukwu, ya bayyana wa Aminiya taskun da ya shiga.

“Kafin yanzu, kusan a ko wanne mako ba a rasa wani buki da za a kira mu kuma masu bukata kan neme mu tun kafin lokacin hidimarsu, amma yanzu babu wanda yake neman mu saboda dokar hana taron jama’a.

“Da ya kamata a ce na halarci bukin aure guda biyu zuwa yanzu, amma hakan bai samu ba.

“Idan ango da amarya da shaidu biyu da kuma pasto sun gayyace ni na halarci bukin aurensu a coci, nawa ne zan samu daga bukin?

“Don haka, abu mafi a’ala a nan shi ne na zauna a shagona maimakon zuwa halartar wani bukin da zai tara mutane da yawa, kafin ’yan sanda su zo su kama ni”.

Lamura ba za su koma yadda suke ba

Shirya gagarumin bukin aure na gani na fada a Najeriya lamari ne da ke lashe miliyoyin dalar Amurka, a cewar TNS Global, wata cibiya mai nazari a kan kasuwanci a duniya.

Aure a Najeriya zai iya lashe $9,460 zuwa $13,515 – gwargwado yanayi da adadin bakin da aka gayyata gwargwadon kudin da za a kasha – inda wasu bukukuwan auren kan samu halartar akalla baki 500.

Amma sakamakon barkewar annobar coronavirus, harkoki da dama sun durkushe.

Masu harkokin da suka danganci bukukuwan auren da muka ambata a baya sun bayyana yadda suke kallon harkokin nasu bayan annobar ta kau an kuma manta da ita.

“Kamar dai yadda muke ji a yanzu, annobar ta zo mana da kalubale iri-iri da kuma bude wasu damammakin a daya bangaren, amma dai yadda abin yake shi ne harkoki suna tangal-tangal saboda su masu bayar da ayyukan ma sun dakatar tukuna, sai dai muna cike da fatan lamuran za su daidaita bayan karkare zaman kullen.

“A matsayinmu na kamfani, muna nan muna ta nazarin halayyar abokan huldarmu da yadda halayyarsu za ta sauya sakamakon shiga yanayin da muke ciki a yanzu – hakan zai taimaka mana wajen fahimtar bukatunsu bayan kare zaman kullen da kuma yadda za mu martaba muradunsu.”

Hauhawar farashi

“Bayan annobar ta kau an kuma manta da ita, akwai yiwuwar samun tashin gwauron zabin farashin kayyaki a kasuwanni.

“Hakan zai faru ne saboda kayan da ake da su a kasuwannin a yanzu, ba za su iya wadatar da bukatun jama’a ba, wannan shi ne gaskiyar lamarin da ya kamata mu fuskanta a nan gaba,” inji Faith Imosemi.

Ra’ayin Ahmed Abdullahi ma ya dace da ma Miss Imosemi.

“Akwai alamu masu karfi da suke nuna lallai za a fuskanci tsadar kayayyakin dab’i bayan wannan zaman kullen.

“Hakan na da nasaba da karancin kayayyakin dab’in daga masu kawo mana su, lura da yadda ba sa iya kaiwa da komawa a tsakanin jihohin kasar nan dalilin haramta zirga-zirga daga jiha zuwa jiha, har sai bayan annobar ta kau.