A Juma’ar nan, 8 ga Dhul-Hajji, 1445 Hijirayye ce ranar farko ta aikin Hajjin bana, inda alhazai kimanin miliyan 1.8 daga sassan duniya za su hadu a Mina domin shirin halartar Tsayuwar Arafa a ranar Asabar.
A wannan rana ta Tarwiyah alhazai suke fitowa sanye da Ihrami suna yin talbiyya da sauran zikirori daga Makkah zuwa Mina gabanin wucewarsu zuwa Filin Arafa.
Tun a daren Alhamis aka fara kwaso alhazan Najeriya zuwa Mina, inda su da sauran alhazai za su yi ibada na kimanin guda, kafin washegari su wuce inda za su halarci Tsayuwar Arafa.
Halartar Tsayuwar Arafa shi ne babban rukunin aikin Hajji, duk alhajin da bai samu ba shi da aikin Hajji.
- Jama’ar gari sun kona gawar dan fashin banki a Abuja
- NAJERIYA A YAU: Shin Mutum Zai Iya Cinye Naman Layyarsa Shi Kadai?
Alhazai za su kasance a Filin Arafa inda ake so su yawaita addu’o’i da zikirori, su kuma saurari huduba daga limaminsu inda bayan hudubar za a hada sallolin Azahar da La’asar a yi su a Kasaru.
Za a kasance a Filin Arafa wuri har zuwa gabin Magariba, inda alhazai za su wuce zuwa Filin Muzdalifa, su yi Sallar Magariba da Isha, su kuma kwana.
Washegari bayan gari ya yi haske za su yi abin da ya sawwaka na addu’a da zikiri a Mash’aril Haram da ke Muzdalifa.
Da hantsi za su koma Mina inda za su yi jifa da aski da yanka hadaya, su cire harami. Wanda ya yi wadannan zai iya yin duk abubuwan da aka hana alhazai yi, in banda saduwar aure.
Wanda ke da dama yana iya zuwa Makka a wannan rana domin gudanar da Dawafin Ifada sannan ya dawo Mina kafin faduwar rana. Shi kuma wanda ya yi wannan, zai iya yin komai, har da saduwar auren.
Alhazai za su kasance a cikin tantunansu da ke Mina har zuwa ranar 12 ko 13 ga wata sannan su dawo Makkah.
Daga nan wanda bai riga ya yi Dawafin Ifada ba zai yi, sai kuma su ci gaba da kasancewa a Makkah har zuwa lokacin dawowarsa, inda a sannan kuma za su yi dawafin bankwana.
Hukumomin Saudiyya sun sanar cewa sun kammala duk shirin da ake bukata domin ganin aikin Hajjin na bana ya gudana cikin aminci da nasara ba tare da matsala.
Hukumomin tsaro da na lafiya da na kwana-kwana da kula da sufuri da kula da muhalli da sauransu sun ba da tabbacin hakan.
A kan haka ne a karon farko hukumar sufurin kasar ta samar da hanyar kasa mai dauke da shimfidar roba domin saukaka wa alhazai masu tafiya a kasa a Mina, Muzdalifa da Arafa.
A nata bangaren, sashen kula da lafiya na Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta shawarci alhazan kasar su yawaita shan ruwa akai-akai akalla lita biyu a kullum, saboda tsananin zafin rana da ake fama da ita a Saudiyya.
Hukumar ta kuma sanar cewa ranar 20 ga wa watan nan na uni za ta fara kwaso alhazanta daga Saudiyya zuwa gida Najeriya.