✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda al’adar gaisuwa ke karfafa zumunci 

Gaisuwa, girmamawa, karramawa, halaye ne masu kyau, kuma ya kamata mu mayar da hankali a kai, don kyautata zamantakewar mu.

Gaisuwa, musabaha, ko sallama wata halayyar dan Adam ce wadda yakan yi ta hanyar yin amfani da wasu kalmomi ko wata inkiya, da sauti ko da wata gabar jiki, da nufin marabtar bako ko sada zumunci da girmamawa. 

Akwai yanayin gaisuwa iri-iri da kabilu ko addinai, da zamantakewa kan sa su rungumi wata halayya ta gaisuwa da nufin mutunta juna.

A wajen wasu al’ummar akan bambanta irin gaisuwar da ake yi wa babban mutum, basarake, ko talaka, mace ko namiji, yaro ko babba.

Nau’ikan gaisuwa

Wasu na gaisuwa ne a tsaye, tare da hada kafadar hagu da ta dama, yayin da hannun dama ke shafar daya bangaren kafadar.

A wajen wasu sai an goga fuskokin juna ko sumbatar wani sashe na fuska.

Akwai kuma masu rungumar juna gaba da gaba ko kuma shan hannu.

Idan basarake ne ko wani mutum da ake girmamawa, wasu kan dunkule hannun dama su yi jinjina tare da dan rusunawa kadan.

Akwai ma masu tsugunawa ko kifuwa a kasa a shimfida jiki.

Duk wadannan nau’o’in gaisuwa ne daban-daban, ya danganta ga kabila ko addini ko kuma nahiyar da mutum ya fito.

Mutane na bai wa gaisuwa matukar muhimmanci, don yadda take karfafa zumunci ko yabawa da kyawun halayya ko tarbiyyar mutum.

gaisuwa
Gaisuwar sarakai a kasar Hausa. (Hoto: answersafrica.com)

Kalaman gaisuwa

Ana kuma jingina gaisuwa da wasu kyawawan kalmomi masu nuni da farin ciki ko kyakkyawan fata.

Kamar irin gaisuwar da Musulmi ke yi ta amfani da kalmomin, Assalamu Alaikum, da kuma gaisuwar Yahudawa ta Shallom ko ta Turawa masu cewa, Hello, ko Good Morning idan safiya ce, ko kuma wani yanayi na cikin yini.

Idan aka yi amfani da kalmomin da ke kunshe a cikin gaisuwa, wadanda ke nuni da aminci da kauna, a tsakanin mai tarba da mai amsawa, ana ayyana cewa, dukkan bangarorin sun bai wa juna ’yanci ta hanyar girmamawa.

Amma idan kalmomin suka bambanta, abin da ake kudurtawa shi ne na cewa, babu cikakkiyar yarda da amincewa.

Tarihin Musulunci ya zo da cewa, a farkon bayyanar sakon ma’aikin Allah Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata gare shi) a garin Makka, kafiran zamaninsa ba sa yarda su mayar masa da kalmomin da ya yi amfani da su na sallama ko gaisuwa da ke nuni da cewa, ‘Amincin Allah ya tabbata gare ku.’

Amma sai su amsa masa da akasin abin da ya ambata, inda suke ce masa, ‘Mutuwa ta tabbata gareka.’ Ma’ana idan ya ce, ‘Assalamu alaikum,’ sai su ce masa ‘Assamu alaika.’

Akwai mutanen da ke daukar cewa, duk wanda ya yi gaisuwa ko ya mayar da gaisuwa ba yadda al’adar mai gaisuwar take ba, to akwai raini ko rashin girmamawa.

Gaisuwa
Yadda ake gaisuwa a al’adar Yarabawa. (Hoto: guardian.ng)

Misali, inda ake gaisuwa a tsugune sai wani ya yi a tsaye, ko ya canza kalmomin da ake amfani da su cikin rashin sani ko da ganganci.

Yayin da ambatar kalmomin ko gaisuwar yadda aka saba kuma aka amince da ita daidai, ko da kuwa ga wanda ya fito daga wata kabila, harshe ko nahiya daban ne.

Wani abu ya taba faruwa a shekarar 2011, yayin da tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya ziyarci kasashen Musulmi a Gabas ta Tsakiya, inda a farkon jawabansa yake farawa da sallama irin ta addinin Musulunci, abin da ya faranta ran da dama daga cikin masu sauraronsa.

Haka ma yayin wata ziyara da ya kai kasar Isra’ila, ya yi amfani da kalmar gaisuwar Yahudawa ta Shallom, abin da ya jawo tafi da sowa mai karfi daga dandazon jama’ar da ke sauraronsa.

Amma a yayin da Obama ya ziyarci kasar Japan inda ake amfani da al’adar rusunawa wajen gaisuwa da girmamawa bayan musabaha ta tafin hannun dama, tsohon shugaban na Amurka ya rusuna wa tsohon Babban Sarkin al’ummar kasar Japan, Akihito, gaisuwar da ta jawo kwakwazo da mita daga wasu manazarta a Amurka da ke ganin wannan rusunawa ba ta dace da shugaban babbar kasa irin Amurka ba.

Wani dan kasuwa ya mika hannu domin musabaha bayan kulla yarjejeniyar kasuwanci. (Hoto: Panorama)

Ka gani ke nan, a yayin da al’ummar kasar Japan ke murna da girmamawar da aka yi wa shugabansu, sai ga shi hakan ya nemi zubar wa da Obama mutunci a idon ’yan kasar sa, saboda ganin hakan da ya yi kaskantar da kimar kasarsa ce a wajen Japan — Ga shi dama kasashen biyu sun taba gwabza yaki a tsakaninsu, lokacin Yakin Duniya na Biyu.

Abin mamaki, sai ga shi kuma an sake kwata shigen hakan a yayin da babban mai arzikin duniyar nan dan kasar Amurka, kuma mai kamfanin manhajar kwamfiyuta ta Microsoft, wato Bill Gates, yakai ziyarar aiki kasar Koriya ta Kudu cikin wannan shekara ta 2013, inda ya gana da tsohuwar shugabar kasar, Park Geun-hye.

Nan ma ga wadanda suke iya tunawa, an yi ta tsagunguma game da yanayin gaisuwar da shigabannin biyu suka yi, inda ’yan kasar Koriya ta Kudu ke korafin cewa, a yayin da tsohuwar shugabar kasar ke musabaha da Bill Gates ta hanyar hada tafin hannun dama, a maimakon attijirin ya nade hannunsa na hagu a baya sai ya soke shi a cikin aljihun wandonsa, abin da ’yan kasar da dama suka fassara da cewa, rashin girmamawa ce da nuna isa ga shugabar kasar tasu.

Idan muka lura da wadannan misalai da na kawo, da ma wasunsu da mai yiwuwa ta taba faruwa a kan idanunka, ko kuma ka ji, za ka yarda da ni idan na ce maka gaisuwa jigo ce mai muhimmanci a zamantakewar al’umma.

Don haka mu kula da kyau, a duk lokacin da muka haɗu da wasu baƙin al’umma, waɗanda al’adunsu da halayyar su ta saɓawa irin tamu, lallai mu lura da yadda suke girmama junansu, da sadar da sallama ko gaisuwa a tsakaninsu ta hanyar yin koyi da su, matuƙar dai bai sabawa imanin mu ba.

Ko da a tsakanin mutane masu addini, akida, da al’ada iri daya, gaisuwa cikin girmamawa tana da matukar tasiri da muhimmanci wajen karfafa alaka da kara wa mutum daraja da kima a idon sauran jama’a.

Nuna girman kai ko fadin rai da wasu ke yi saboda tunanin sun mallaki wata dukiya ko matsayi a cikin al’umma, babban kuskure ne, kuma yana sanya katanga da nesanta mutum daga samun duk wata alfarma da zai iya nema ko bukata.

Gaisuwa, girmamawa, karramawa, halaye ne masu kyau, kuma ya kamata mu mayar da hankali a kai, don kyautata zamantakewar mu.

Hakan zai kara mana mutunci, aminci, da yarda a tsakaninmu.

Sallama na raunana zuciyar da kiyayya da tsana suka yi wa katutu.

Salamu Alaikum!

Abba Abubakar Yakubu, ya rubuto wannan makala ne daga Jos

imel: [email protected]