✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin miyar wake

Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya kamar kullum. A yau na kawo muku yadda ake miyar wake. Wannan miyar al’adace…

Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya kamar kullum. A yau na kawo muku yadda ake miyar wake. Wannan miyar al’adace ta Nufawa kuma suna yawan yin ta a gida ko kuma a taron bukukuwa da sauransu. Suna kiran miyar da suna ‘Ezowa’ wato miyar wake. Yana da kyau uwargida ta koyi girke-girke na kabilu daban-daban domin hana maigida cin abinci a waje, da kuma sanya kunnensa motsi. Anfi hada wannan irin miyar da tuwon shinkafa.

 
Abubuwar da za a bukata
• Wake
• Man ja
• Attarugu
• Busasshen kifi
• Albasa
• Gishiri da magi
 
Hadi
Idan uwargida ta samo wakenta, sai ta jika. Bayan hakan, sai ta cire kowar jikin waken. Sai ta daura ruwa a wuta. Bayan ya tafasa, sai ta zuba waken ya yi ta tafasa har sai ya nuna ya yi lugwi. Sannan sai ta zuba yankakkiyar albasa da dakakken attarugu da manja da busasshen kifi. Sai a jira miyar ta yi ta tafasa na mintuna kadan, sannan sai a zuba magi da gishiri. Hhmmn!  Lagwada! Ana iya cin wannan miyar ne da tuwon shinkafa. Kuma anfi son amfani da ita da rana ko da yamma. Lallai idan maigida ya ci wannan abincin sai kunnensa ya motsa. Da fatan za a girka wa maigida wannan miyar domin armashi da kuma dandano mai gamsarwa!