A Jihar Kebbi sama da kwana 100 na sabuwar gwamnati, idan aka cire Gwamna, akasarin manyan mukamai a jihar duk na rikon kwarya ne. Manyan mukamai da suka hada da kwamishinoni da manyan sakatarorin ma’aikatu, shugabannin kananan hukumomi da wadansu hakimai da dagatai duk a rikon kwarya ake tafiyar da su.
Sauran wadanda suke rikon kwaryar sun hada da Shugaban Ma’aikata da Babban Joji da sauransu da dama.
Aminiya ta gano cewa, baya ga rashin nada kwamishinoni da yanzu haka a Jihar Kebbi akwai gurabun manyan sakatarori 10 da ba a nada ba, inda manyan daraktoci a ma’aikatunsu suke riko, lamarin da yake kawo tafiyar hawainiya ga gudanar da ayyukan gwamnati, haka lamarin yake a kananan hukumomi inda babu zababbu ko nadaddun shugabanni, sai dai na riko.
Wadansu masana sun shaida wa Aminiya cewa rashin nada wadannan mukamai na iya kawo wa ma’aikatun gwamnatin jihar koma-baya da kuma jefa ma’aikata cikin mawuya cin hali.
Haka kuma jama’a da dama a jihar suna nuna damuwa kan yadda aka share sama da kwana 100 da rantsar da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu karo na biyu kan mulki amma har yanzu bai nada ’yan Majalisar Zartarwar Jihar ba, wato kwamishinoni, alhali wadansu gwamnoni hatta sababbin kamu a wasu jihohin tuni suka rantsar da nasu suka kama aiki.
Wani babban ma’aikaci jihar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce: “Gaskiya ce wadansu manyan sakatarorin wasu ma’aikatun gwamnatin jihar na rikon kwarya ne. Saboda haka a iya nawa sanin shi ne, yanzu haka ana kan tantance sunayen wadansu da za a tabbatar da su a matsayin manyan sakatarori a ma’aikatun gwamnatin jihar.”
Ya ce irin wannan aiki na tantancewa yana daukar lokaci ana yin sa. Kuma ya ce, “Rashin nada Shugaban Ma’aikata yana da nasaba da cewa wanda ke rikon kwarya a halin yanzu ba zai kai shekara daya yana aiki ba zai yi ritaya daga aikin gwamnati saboda lokacinsa na ritaya daga aiki ya karato. Bisa ga haka ne nake tunanin cewa yana daya daga cikin abin da ya sa ba a tabbatar da shi a matsayin Shugaban Ma’aikatar Jihar ba, sai dai a matsayinsa na wanda shi ne mafi girma a cikin manyan sakatarori a ma’aikatun gwamnatin Jihar Kebbi, wato Alhaji Musa Tanko Magaji. Saboda haka a matsayina na daya daga cikin manyan ma’aikatan jihar, ina sa ran cewa wannan dalilin da na bayyana na iya zamowa dalilin da suka sa ya kwashe watanni yana rikon kwarya ba tare da an tabbatar da shi cikakken Shugaban Ma’aikata ba.”
Lokacin da wakilinmu ya zanta da wani babban lauyan gwamnati, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, “Gidan shari’a wuri ne da ake bin doka da oda saboda haka a dokar gidan shari’a, za a bai wa duk alkalin da shi ne kan gaban ga kowane alkali, shi ne zai yi rikon kwarya a matsayin Babban Jojin Jihar har zuwa wata uku ko wata shida kafin tabbatar da shi a matsayin Babban Jojin Jiha. Zan ba da misali da Babban Jojin Najeriya, ai sai da ya yi rikon kwarya na wata shida kafin Fadar Shugaban Kasa ta aike da sunansa zuwa Majalisar Dattawa don tantance shi. Haka ne yake a kowace jiha ta kasar nan. Saboda haka a nan Gwamnatin Kebbi ba ta saba wa doka ba, ta yi abin da dokar kasa ta tanada ce.”
A makon jiya ne Gwamnatin Jihar Kebbi ta shirya bikin cikar jihar shekara 28 da kirkirowa, inda ta gayyaci duk ’yan asalin jihar na cikin gida da na wajen kasar nan don a hadu domin tattaunawa da ba da shawarwari kan yadda za a kara samar da ci gaba mai amfani ga jama’ar jihar da kuma kara inganta ita kanta jihar.
A wurin taron ne Farfesa Bello Aliyu Bada da ke Sashen Nazarin Ingilishi da Harsunan Afirka a Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato, ya bayyana kokensa kan yadda mukaman gwamnatin jihar suke tafiya a kan rikon kwarya.
A kan haka ne ya ba da shawawar cewa Gwamnan Jihar, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya gaggata nada mukamai domin aikin gwamnati ba ya tafiya sai da ma’aikata.
A jawabansa a wurin taron, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana cewa “Ba da jimawa ba gwamnati za ta tabbatar da cewa ta nada ’yan Majalisar Zartarwar Jihar wato kwamishinoni. Kuma za ta nada manyan sakatarori da sauran mukaman da ake ganin aikin gwamnatin ba ya tafiya sai da su.”
Ya ci gaba da cewa, “Ni daya ba na iya mulkin Jihar Kebbi, dole sai tare da ku jama’ar Jihar Kebbi, ta hanyar ba ni shawarwari da kuma taimaka wa gwamnatin a wuraren da ake ganin bai yi ba, don ta iya gyarawa ko canja tsarin da ta dauko, wanda ake ganin cewa bai yi daidai da ra’ayin jama’ar jihar ba. Amma duk wannan ba zai iya samuwa ba sai in akwai hadin kai a tsakanin juna da kuma mutuntawa, sannan ne kawai za a iya cimma abin da ake so.”
Daga nan ya ce Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin jagorancinsa, za ta yi iya kokarinta don ganin ta ayyana abubuwan da jama’a ke so.
A bangaren sarautun gargajiya wato hakimai da dagatai Aminiya ta gano akwai gurabu kusan 50 da duk na riko ne, lamarin da ya sa jama’ar jihar da dama suke kokawa kan yadda har yanzu wadansu hakimai rikon kwarya suke yi. Binciken Aminiya ya gano a masarautar Yawuri cikin hakimai 15 akwai guda na riko, sai dai akwai dagatai da dama na riko a masarautar kamar yadda wata majiyar fadar Sarkin Yawuri ta tabbatar wa Aminiya. A masarautar Zuru wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa babu hakimi mai rikon kwarya, amma akwai dagatai da dama da suke rikon kwaryar da majiyar ba ta iya tantance adadinsu ba.
Sannan wani mazaunin masarautar Argungu mai suna Abdul Nasir ya tabbatar wa Aminiya cewa akwai hakimai da dagatai na rikon kwarya.
Da Aminiya ta tuntubi Masarautar Gwandu, wani babban dan Majalisar Masarautar wanda ya nemi a sakaye sunansa, Ya ce “Lallai akwai hakimai da dagatai da suke rikon kwarya a masarautar, to amma ba zai iya yin wani karin bayani a kan lamarin ba, domin ba a ba shi izinin yin haka ba.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Gwamnan Jihar kan wannan korafi ya ce ba zai iya cewa komai a kan lamarin ba, sai dai a tuntubi Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Baballe Umar. Sai dai kuma da Aminiya ta tuntube shi sai aka shaida mata suna yin wata tattaunawa kuma har zuwa hada wannan rahoto a jiya Alhamis ba su kammala ba.