✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liverpool ta shiga zawarcin Rodrygo

An fara raɗe-raɗin Liverpool na son kawo Marcus Rashford daga Manchester United.

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta shiga zawarcin ɗan wasan gaban Real Madrid, Rodrygo Goes wanda aka sanya wa farashin euro miliyan 100.

Wannan dai na zuwa ne yayin da takwararta ta Ingila, Arsenal ke neman ɗaukar ɗan wasan na ƙasar Brazil.

Tuni Liverpool ta shirya tattaunawa da wakilan ɗan wasan, wanda tun da fari aka bayyana cewa yana shirin barin Madrid sakamakon rashin samun gurbi ƙarƙashin sabon koci Xabi Alonso.

Liverpool dai na neman sabon ɗan wasan gaba don ƙarfafa tawagarta bayan lashe kofin Firimiya a Ingila na kakar 2025-26.

Sai dai kafin Liverpool ta shiga zawarcin Rodrygo a kasuwar cinikin ‘yan wasa ta bazarar nan, Arsenal da Bayern Munich suna cikin masu neman ɗauko tauraron.

Bayan Rodrygo, akwai wasu taurarin da Liverpool ke fatan ɗaukowa, irinsu Alexander Isak daga Newcastle da Hugo Ekitike daga PSG ta Faransa.

Ko a makon nan ma, an fara raɗe-raɗin Liverpool na son kawo Marcus Rashford daga Manchester United.

Sai dai a halin da ake ciki, farashin da Real Madrid ta gindaya wa Rodrygo ya kai euro miliyan 100 (wato dala miliyan 106), wanda masu sharhi kan wasanni ke ganin ya yi tsada sosai.