Hukumar kula da hada-hadar hannayen jari a Nijeriya SEC ta ce ta soma bincikar kamfanoni masu shirin damfarar mutane ta hanyar yi musu alkawarin ninka musu jarin da suka zuba da ake kira ponzi schemes guda 79 da ke aiki a fadin Nijeriya.
Hukumar ta ce cikin wadanda ake binciken har da wani kamfani mai suna FF Tiffany wanda take zarginsa da zambatar masu zuba jari kuma ya yaudari dubban ’yan Nijeriyar a ciki da wajen kasar.
BBC ya ruwaito hukumar ta SEC tana alkawarin bayyana sakamakon binciken ga jama’a.
- Yadda za a ci gaba da zaman karɓar gaisuwar Buhari
- Hauhawar farashi ya sauka zuwa kashi 22.22 a watan Yuni — NBS
Kazalika, ta kuma bayyana irin wadannan yaudara a matsayin barazana ga yadda da amincewar mutane a fannin hada-hadar kudi ta ƙasar wanda kuma zai rage kwarin-gwiwar masu zuba jari.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta na kawar da duk wani shirin yaudarar mutane da kwashe musu kuɗaɗensu a Nijeriya.
Ta kuma ce ’yan Najeriya za su iya ziyartar shafinta na intanet domin tabbatar da sahihancin duk wani kamfanin zuba jari kafin su sanya kuɗadensu.
Sai dai baya ga haka kuma, hukumar ta ce ta soma shiga lungu da sako na ƙasar kamar manyan kasuwanni da wuraren ibada domin wayar da kan jama’a kan yadda za su kaucewa irin wadannan masu yaudarar.
Hukumar ta kuma ce a cikin shekarar nan shugaban Kasar Bola Tinubu ya sanya hannu kan wata doka wadda ta bayar da damar cin tarar duk wanda aka kama da hannu a irin waɗannan shiri, naira miliyan 20 ko kuma zaman gidan yari na shekara 10.
Sai dai wasu masana a fannin tsaron naurar intanet na ganin akwai bukatar gwamnati ta rubanya kokarin da takeyi domin har yanzu al’umma na fadawa tarkon masu irin wadannan shirye-shirye.
Ko a cikin watan Afrilun wannan shekara, ’yan Najeriya sun tafka asarar kuɗi a wani tsarin zuba jari mai suna CryptoBank Exchange wanda aka fi sani da CBEX da ya kai aƙalla naira triliyan daya.
Duk da wasu hukumomin ƙasar sun ce suna binciken lamarin domin gano masu hannu a ciki, kuma zuwa yanzu sun gano wasu daga cikinsu, sun ce da wuya su iya dawowa kowa da kudinsa.