Shugaban ’yan bindigar da suka sace dalibai 344 a Makarantar Sakandaren da ke Kankara a Jihar Katsina, Awwalu Daudawa ya ce saukin samun makamai a gare su tamkar sayen burodi ne.
A hirarsa ta musamman da Aminiya, Auwalu Daudawa ya bayyan yadda shi da yaransa suka kai ga daukar makamai, har suka wayi gari suna garkuwa da mutane.
- Sunayen dalibai da malaman da aka sace a Makarantar Kagara
- An kama kwamandan Hisbah da matar aure a dakin otel a Kano
- Makarantar Kagara: Atiku ya bukaci a ba sojoji tsaron makarantu
- Matashi ya kashe kansa ta hanyar guntule al’aurarsa a Kano
“Ka tara dukiyar da kake gani …za ka ciyar da gidanka, an tura jami’an tsaro sun kore, ya zan yi ke nan da rayuwata kuma ga ni da yara ga matana. Kasa zan ci?
“Na je na harhada kadarata na sayi makami na shi wannan harkar [ta ’yan binida].
A hirarsa da Aminiya ’ya makonni bayan ya bayyana tubarsa da yaransa tare da mika wa Gwamnatin Jihar Zamfara makamai, Daudawa ya ce sayen mamakai a wurinsu “kamar yadda za a sayi biredi ne a gare mu.”
Cikakken bayanin abubuwan da ya fada har da bidiyon na nan tafe a shafin Aminiya a karshen mako.
A cikin hirar ya bayyana yadda suka fara garkuwa da mutane da abin da ya sa suka yi garkuwa da daliban Kankara da tubarsa da wasu muhimman batutuwa.