Yadda ake miyar kaza da dankali turawa (Chicken curry with peas and potatoes sauce) wadda ake iya ci da a farar shinkafa ko ita kadai.
Kayan Hadi
– Kaza
– Wake (peas)
– Garin curry
– Gishiri
– Kayan dandano
– Tumatiri
– Koren tattasai
– Bakin barkono
– Tafarnuwa
– Citta
– Albasa
– Man gyada
– Dankali turawa
– Ruwa
– Shinkafa
Yadda ake hadin
1. A yanka kaza kana a cikin kwano a hada da yankakken tumatir, gishiri, bakin barkono, dakakken koren tattasai, sinadarin dandano, citta, da yankakken tumatir.
2. A kwaba da kyau a saka cikin firinji na minti 30.
3. A sa mai, albasa da aka yanka da tafarnuwa, a tukunya mai a soya an kamar minti uku sai a zuba garin curry isasshe, sannan a kara dafawa a minti uku zuwa hudu, a kan wuta ba mai yawa ba.
3. A zuba kazar a ciki, a yi ta juyawa akai-akai, har zuwa kaman minti biyar zuwa bakwai.
4. A zuba ruwa a kwano da kika dafa kazar a ciki domin debo sauran kayan dandano.
5. A kara dankalin turawa a da wake (peas) a ciki sai a kara ruwa, a bar shi a wuta har sai ya yi laushi da kauri sosai.
6. Idan miyar ba ta yi kauri ba, sai a yi amfani da bayan ludayin miya a murkushe waken da dankalin, zai yi kauri.
7. A karshe sai a zuba ganyen parsley a juya, miya ta nuna sai ci.
Ana iya cin miyar da farar shinkafa da kuma ko ma ita kadai.