✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake kula da zakuna a Gidan Zoo na Jos

A lokacin da wakilinmmu ya ziyarci Gidan Zoo na Tarayya da ke Jos a Jihar Filato, bangaren da aka kebe zakuna, ya gan su cikin…

A lokacin da wakilinmmu ya ziyarci Gidan Zoo na Tarayya da ke Jos a Jihar Filato, bangaren da aka kebe zakuna, ya gan su cikin katon kejin da aka yi shi da wayoyi masu kauri don killace su.

Aminiya ta gano akwai zakuna biyar, maza uku da mata biyu, inda a kwanakin baya aka haifi wata zakanya.

Aminiya ta nemi jin ta bakin Manajar Gidar, amma abin ya ci tura, sai dai wata majiya mai tushe ta ce ana kashe Naira dubu 30 wajen ciyar da zakunan a duk lokacin da za a ciyar da su.

Majiyar ta ce ba kowace rana ake ciyar da zakunan ba, “Amma duk ranar da za a ciyar da su nama, to za a kashe Naira dubu 30. Ba kowace rana ake ciyar da su ba, domin idan sun ci sun koshi to naman yakan dauki tsawon awa 24 ko 48 kafin ya narke, don haka zakunan ba za su bukaci abinci ba, inda hakan ya sa wani lokaci ake tsallaken kwana daya ko biyu kafin a sake ciyar da su, wani lokaci kuma akan ciyar da su sau uku a mako.”

Majiyar ta ce idan aka yi rashin sa’a wani daga cikin zakunan ba ya da lafiya, to bayan an binciko cutar da ke damunsa, sai a sanya maganin a cikin naman da za a ba shi, idan kuma dabba mai rai kamar rago za a ba shi, sai a yi wa dabbar allurar maganin, inda idan zakin ya ci sai maganin ya bi jikinsa ya kuma warke.

“Ba a ba zakunan dafaffe ko soyayyen nama, danyen nama ake ba su, kuma idan suka koshi shi ke nan, sai su yi ta shakatarwarsu. Amma idan ka ji zakuna suna kuka, to suna jin yunwa ko ba su da lafiya, idan suka dade ba su ci abinci ba muka ji suna kuka, to mun tabbata yunwa ce, idan kuma bayan an ba su abinci aka ji suna kuka, to akwai wata matsala, sai mu bincika don magance ta,” inji majiyar

Majiyar ta ce biyu daga cikin zakunan mace da namijin da suke haihuwa sun fi shekara 10 a gidan, “Ka ga an dauke ni aiki a gidan namun dajin nan fiye da shekara 10, to ni ma haka na gan su da girmansu, amma na taba tambayar wani da ya ce mini namijin da aka fara kawowa ya kai shekara 25, amma ban tabbatar ba,” inji majiyar.

Majiyar ta ce ba ta taba samun matsala da wani daga cikin zakunan ba, duk da cewa tana daga cikin masu ba su abinci.