✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake jus din gurji mai zobo

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na girke-girke tare da fata ana cikin koshin lafiya. Yana da kyau a san yadda…

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na girke-girke tare da fata ana cikin koshin lafiya. Yana da kyau a san yadda ake yin nau’ukan girke-girke da kuma mahadinsu. Ina nufin jus ke nan. Duk dadin abinci yana bukatar mahadi da zai dada wa girkin armashi. Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake wata mahadar girki; jus din gurji.

Abubuwan da ake bukata

• Gurji

•Kankana

•Ayaba

• Lemu

• Amfuna

• Gwanda

• Zobo

• Flaba

• Sakari

• Citta 

• kanumfari

Hadi

A sami gurji kamar goma sai a fere sannan a markadasu a na’urar markade a tatse ruwan a ajiye a gefe. A sami kankana a yayyanka kanana sosai a wata roba da ayaba da amfuna da gwanda duka a yayyankasu kanana sannan a ajiye a gefe.

A tafasa zobo da kayan kamshi kamar su citta da kanamfari da kuma bawon abarba. Sannan a tafasa sosai sannan a tace a ajiye ya huce sannan a zuba sukari da flaba sannan a sanya a gidan sanyi.

Bayan haka, a debo wannan ruwan gurjin a zuba a zobon sannan a zuba wadannan yankakken ’ya’yan itatuwan a zubasu a kofi sannan a zuba wannan jus din zobon. Ana sha ana tauna.