’Yan ta’addar ISWAP sun tarwatsa wata gada da ta haɗa garin Ngirbuwa da garin Goneri a Ƙaramar Hukumar Gujiba da ke Jihar Yobe.
Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda da ‘yan ta’addan suka lalata gadar nan ta Mandafuna da ta haɗa garin Biu da Damboa a Jihar Borno.
- JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana
- Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi
Majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa harin ya afku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ta hanyar amfani da wani bam wajen lalata sauran sassan gadar.
Wannan aikin ta’addanci ya kawo cikas ga zirga-zirga tsakanin al’ummomin biyu da ma sauran al’ummomin yankin, lura da cewar gadar na kan hanyar Katarko ne zuwa garin Goneri.
Masana tsaro na nuna cewar, lalata wannan gadar mota na iya kawo cikas ga harkokin tsaro a wannan yanki, lura da cewar yankin na da iyaka da wasu dazuzzukan da ke da iyaka da dajin Sambisa da ya zama maɓoyar ‘yan ta’addan a wasu ɓangarorin.