✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas

Cikin gawawwakin mamatan biyar da aka samu akwai mata uku da maza biyu.

Kawo yanzu an samu aƙalla mutum biyar da suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar ruftawar wani bene mai hawa uku da ya ruguje a unguwar Ojodu-Berger da ke Jihar Legas.

Haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe 09.45 na safiyar ranar, inda hukumar kai ɗauki gaggawa tare da taimakon ’yan sanda suka gano cewa wani gini mai hawa uku ɗauke da gidan abinci da mashaya ne ya ruguje.

Jami’in hukumar bayar da agajin, Ibrahim Farinloye, ya ce daga faruwar lamarin zuwa yanzu an ceto mutane 20 jimilla da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai.

“Sai dai abin takaicin shi ne cikin gawawwakin mamatan biyar da aka samu akwai mata uku da maza biyu.”

Shi ma da yake nasa jawabin a ranar Lahadi, babban Sakataren hukumar LASEMA, Olufemo Oke-Osanyintolu, ya ce mamatan biyar da aka samu an killace su a ɗakin ajiyar gawawwaki na asibiti.

Da farko dai babu labarin mutuwa, sai dai an samu asarar dukiya, amma yanzu bayan ci gaba da aikin ceto, an gano gawawwaki a cikin waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai.

’Yan sanda da hukumar kai dauƙin gaggawa sun ci gaba da bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin.

Jami’ai na hukumar LASEMA na ci gaba da binciken baraguzan ginin da nufin gano ko da sauran mutane a ciki.