Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya shawarci Kanawa kan kada su bari bambance-bambancen aƙidu na siyasa su zama silar hana su zaman lafiya da haɗin kai.
Ya faɗi hakan ne a jawabinsa lokacin da ya je yi wa Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ta’aziyar rasuwar mahaifinsa — Galadiman Kano, Abbas Sunusi.
- Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu?
- An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi
Shettima ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai, yana mai bayyana Kano a matsayin madubin Arewacin Nijeriya.
Yayin da yake nanata muhimmancin zaman lafiya, ya bayyana cewa kada a yi sake da Kano, inda ya buga misali da yadda rashin zaman lafiya ya ɗaiɗaita Jihar Borno.
Shettima ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a fannin siyasa da su ajiye banbancin aƙidu, su bai wa ci gaban Kano fifiko a kan komai.
Ya tunatar da cewa Jihar Kano wata cibiya da kusan duk jihohin Arewa suka kewaye kuma ta zama tamkar wata ƙofa da ta zama mahaɗar jihohin
“Idan za ka je Borno ko Bauchi ko Sakkwato, dole ne sai ka bi ta Kano. Saboda haka Kano jiha ce ta kowa.
Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya yi Mataimakin Shugaban Ƙasar rakiya a yayin ziyarar ta’aziyyar da ya kai gidan marigayi Galadiman Kano.