Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan fili namu na girke-girke.
A yau na kawo muku yadda ake dahuwar kwai a cikin nama.
Har ila yau ina dada ba ku shawara a kan girki mai armashi wanda zai sanya maigida ya manta hularsa da kuma hana shi cin abinci a waje.
Domin sauya irin nau’o’in abinci a koyaushe shi ya sa na kawo muku wannan sabon salon girkin. A ci dadi lafiya.
Abubuwan da za a bukata sun hada da:
- Kwai
- Ruwan qwai
- Fulawa
- Magi
- Garin busasshen burodi
- Nama/ ‘sausage
- Kori
- Man gyaxa
Hadi
A tafasa kwai har sai ya nuna sannan sai a bare.
Bayan haka, sai a samu ‘Sausage’ a kwaba shi da cokali.
Daga nan sai a wanke hannu a goge.
Sannan a zuba man gyada kadan a tafin hannu a dora nikakken naman sannan sai a shafe shi a tafin hannu.
A dauko dafaffen kwan sannan a lullube shi.
Bayan haka, sai a fasa kwai a zuba madaran ruwa kadan ko nono a kwaba, sannan sai a tsoma kwan a ciki.
Sai a samu fulawa a yaryada mata magi da kori a gauraya su sannan a saka kwan a ciki yadda fulawar za ta rufe kwan tsaf.
Bayan haka, sai a sake tsoma kwan a cikin ruwan kwan. A tsame sai a saka a cikin garin busasshen burodin yadda garin burodin zai lullube shi.
A zuba man gyada a wuta bayan ya yi zafi, sai a soya.
Sannan a tsame a sha da shayi.