✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MAGGI: Girke-girken Ramadan masu kawo sauyi da zumunta

lokaci ne na inganta rayuwa da Lokaci ne kuma na bayar da labarai na nishadantarwa da zumunta da kuma jin dadin kasancewa tare

Ramadan lokaci ne da ke hada kan iyalai da al’ummomi a fadin duniyar Musulmi. Lokaci ne da masoya ke haduwa tun daga lokacin sahur har zuwa buda-baki, ta hanyar kasancewa tare domin cin abinci mai gina jiki.

A wannan lokacin, ba a yin abinci don nishadi kawai, lokaci ne na inganta rayuwa da bayar da labarai na nishadantarwa da zumunta da kuma jin dadin kasancewa tare.

A cikin wannan labari mai ban sha’awa na MAGGI mai taken Labarin Ramadan, wasu mata biyar sun yi tafiya ta tsawon wata guda don samar da sauye-sauye, inda suka gano hadaddun girke-girke na sada zumunta da ke da alaka da samar da labarai masu jan hankali, har guda shida.

Tare da wasu jaruman wasan kwaikwayo da suka hada da Rekiya Attah, Labaran MAGGI na Ramadan suna kunshe da labarai masu kayatarwa, kuma masu dadi har na tsawon mako shida da aka fara tun farkon wannan watan na Ramadan. Wannan yanayi ya zame wa kowa jiki, to amma ya fi dadi a yayin da muka hadu a matsayinmu na iyali ko al’umma a lokacin Ramadan.

Kowane bangare na labarin yana nuna ainihin yadda lokacin Ramadana yake, ta fuskar son juna da zumunci da kuma yadda ake samun gamsuwa a lokacin buda-baki. Ta fuskar lokutan fahimtar juna da ba a yi tsammani ba ake yaukaka dangantaka da tabbatar da cewa, abokantaka tamkar tsintsiya ce madaurinink daya, inda take kawo kwanciyar hankali da annashuwa har ma a lokutan da ake cikin tsanani.

Da take magana a kan kudirin MAGGI na karfafa danganta da abokan huldasa a lokacin Ramadan tsawon shekara goma da suka gabata, Manajan Girki ta Kamfanin Nestlé Nigeria, Misis Rahamatou Palm-Zakari ta ce, “Ramadan lakaci ne na kyauta da soyayya, wanda MAGGI yake jaddadawa. Ta hanyar ci gaba da gabatar da samfuran da girke-girkenmu masu farin jini da samar da labaran Ramdan a yanzu, mun sadaukar da kanmu wajen ci gaba da yin kyakkyawan tasiri a rayuwar abokan huldarmu. Ta hanyar kayayyakin da muke samarwa da dandadon girki, za mu ci gaba da tallafa wa daidaikun mutane da iyalai wajen zabin abinci mai dandano da kara lafiya a kowace rana.

A matsayin kamfani da ya kudiri aniyar hada kan mutane ta hanyar abinci, MAGGI ya yi imani da muhimmancin burin samun abinci mai dandano.

MAGGI wani bangare ne na Kamfanin Nestlé, wanda kamfani da yake samar da abinci mai dandano da kyakkyawar rayuwa da ya kudiri aniyar bayyana irin rawar da abinci yake takawa wajen inganta rayuwa kowa da kowa a yanzu da kuma zamani mai zuwa.