✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — Fulani

A wajen Fulani Jahunawa na jihar Jigawa, cin naman akuya na haifar da ciwon mara (Kaba).

Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, wasu Fulani daga Karamar Hukumar Jahun ta Jihar Jigawa sun yi imani cewa, idan suka ci naman akuya, maza za su kamu da cututtukan da suka shafi maraina, musamman ciwon mara da aka fi sani da ƙaba ko kumburin maraina, yayin da mata kuma za su kamu da ƙuraje a fatar jikinsu.

Malam Aminu Muhammad Jahun ya shaida wa wakilinmu cewa, tun yana yaro yake guje wa cin naman akuya, yana mai bayyana cewa, yawancin Fulani a yankinsu ba sa cin naman akuya, kuma idan aka ci, za a kamu da ciwon ƙaba.

“Mu dai muna kiwon akuya a wannan al’umma, amma ba ma cin namanta. Maimakon haka, muna sayar da su ne.

“A gaskiya, akwai doka a danginmu da ke hana kowa cin naman akuya cikin gidansa.

“Cin naman akuya wani abu ne da ba a yarda da shi ba a kauyenmu.

“Wannan al’ada ce da muka gada daga kakanninmu, kuma har yanzu muna kiyaye ta a cikin iyali.

“Wannan al’ada ta daɗe, ba mu ma san lokacin da ta fara a yankinmu ba.

“Mun tashi kawai muka ga iyayenmu suna yin hakan, mu kuma muka ci gaba,” in ji Muhammad.

Naman akuya na haifar da ƙuraje — masu cin naman

Jihar Sakkwato tana ɗaya daga cikin jihohin Arewacin Nijeriya da ke taka rawar gani wajen kiwon dabbobi.

Ana kiyasta cewa, jihar na da jimillar awaki miliyan 2.9 da shanu miliyan 3.4 da tumaki miliyan 1.9 da jakuna 40,000.

Sai dai duk da irin gudunmawar da jihar ke bayarwa wajen samar da dabbobi da kuma yadda mutanenta ke son cin nama, yawancin Fulani a Sakkwato ba sa cin naman akuya.

Jaridar Aminiya ta lura cewa, ba za a iya samun naman akuya da aka dafa ko aka soya a tukuba ko gidajen abinci da otal-otal a cikin babban birnin jihar ba.

Haka kuma ba kasafai ne mutanen Sakkwato ke yanka akuya a lokacin bukukuwan sallah ko suna ko bukukuwan aure ba.

Saboda wannan al’ada, yawancin awakin da ake samarwa a Sakkwato ana tura su ne zuwa Kudu maso Yamma da wasu makwabtan jihohi kamar Kano da Katsina da Kaduna domin a ci namansu a can.

A sakamakon haka, kadan daga cikin awakin da ake sarrafa su a cikin babban birnin jihar suna zuwa ne ga kabilun Yarbawa da Igbo da Egbira.

Tasirin wannan doguwar al’ada ya fi fitowa a cikin birane fiye da karkarar jihar Sakkwato.

Malam Ibrahim Auwal, wani mai sana’ar saye da sayar da dabbobi a kasuwar dabbobi ta Ƙofar Dundaye a Sakkwato, ya tabbatar da cewa, yawancin awakin da ake kawowa kasuwar ana tura su ne zuwa wasu jihohi don a siyar a can, yana mai cewa “mutanenmu nan Sakkwato ba sa cin naman akuya.”

“Fiye da kashi 90 cikin 100 na awakin da ake kawowa nan, ana tura su ne zuwa Kudu.

“Kashi 10 kawai ake sayarwa a cikin babban birnin jihar da kewaye.”

Da yake magana da wakilinmu ta wayar tarho, Alhaji Habibu Musa, wanda yake yanka dabbobi a kasuwar kara ta Sakkwato, ya bayyana cewa, saboda karancin cin naman akuya a Sakkwato, ana yanka awaki kadan ne a mayankarsu.

“A rana guda, ba mu yanka fiye da akuya 10 zuwa 15 ba saboda ba a cin naman akuya sosai a birnin Sakkwato.

“Duk da haka, Fulani da suke zaune a kauyuka kamar Bodinga da Gwadabawa da Illela da Dundaye da Dange da sauran kananan garuruwa suna cin naman akuya kuma ba su da wata matsala.

“Don haka, dan naman akuya da ake yankawa a nan yana zuwa wuraren nan don a ci.”

Wani mazaunin Sakkwato, Malam Bala Idris ya bayyana cewa, “a cikin iyalina, ba ma cin naman akuya, domin yana haifar mana da cutar fata, wadda muke kira Sameha wato ƙuraje a harshen Hausa.

“Ba wani daga iyalina da ke cin naman akuya. Haka muka tashi da wannan al’ada kuma muka ci gaba da ita. Matata da yara ma ba sa ci.”

Al’adar na ƙara raguwa

Wani babban jami’i a kafar yada labarai. wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, yana sane da al’adun Fulani na kauce wa cin naman akuya, inda ya ce, “na san wannan al’adar, amma ina ganin tana raguwa a birane.

“Yawancin lokaci, akuya ana kallon ta a matsayin dabba mara kima idan aka kwatanta da saniya ko rago. Amma gaskiya al’adar tana canzawa.

“Ni kaina ina cin naman akuya. Ina ganin a birane mutane suna barin wadannan tsoffin al’adu na Fulani,” in ji shi.

Me ya sa ba a cin naman akuya?

Kabiru Zubairu, wani matashi Bafullatani da ke zaune a Dukku, Jihar Gombe, ya bayyana ra’ayinsa kan wannan al’ada ta kauce wa cin naman akuya.

Ya ce: “A ganina, akwai dalilai guda biyu da suka sa haka: na farko, an samo shi daga al’adar Fulani ta rashin cin naman akuya.

“Na biyu kuma, akwai wani tunani cewa, cin naman akuya na iya haifar da cuta, wadda ake kira saɗaure a harshen Fulfulde, wato yana kallon nama a matsayin mara kyau ga lafiya.

“Wannan tunanin har yanzu yana nan, yadda na sadaukar da akuya a lokacin babbar sallar na iya zama muhawara a tsakanin Fulani.

“Wannan yana nuna cewa, tunanin rashin cin naman akuya ya tsaya sosai.

“Amma idan akwai Fulani da ke ci yanzu, yana iya zama sakamakon tasirin zamansu a birane.”

Kabiru ya ƙara da cewa, wasu abubuwan zamantakewa, kamar auratayya tsakanin ƙabilu daban-daban, suna iya taimakawa wajen sassauta wannan al’ada.

Naman akuya ba ya cutar da lafiya

Sai dai Malam Salisu Maiwanki, wani Bafulatani daga Ƙaramar Hukumar Shira, Jihar Bauchi, yana cin naman akuya kuma ba ya cutar da shi.

Ya ce, “ni da iyalina, muna cin naman akuya kuma ba mu da wata matsala.

“A gaskiya, muna cin dukkan nau’o’in nama ba tare da fuskantar wata matsala ta lafiya ba.”

Dakta Lamaran Mansur, likita a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ya bayyana cewa, wannan tunanin cewa naman akuya na cutarwa ba daidai ba ne a kimiyyance.

Ya ce, “wannan kawai tunani ne wanda ba a tabbatar da shi a kimiyyance ba a duniya.

“Naman akuya yana dauke da sinadarin protein mai yawa da kananan kitse, wanda ke da amfani sosai ga lafiya.”

Ya ƙara da cewa, idan gwamnati za ta ba da ilimi mai kyau kan wannan batu, za a iya cire wannan tunanin kuma mutane za su amfana da wannan nama mai albarka.