✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta kama matashi yana ‘baɗala’ da Akuya a Kano

Matashin ya bayyana nadamarsa yana mai cewa ba zai ƙara ba.

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta cika hannu da wani matashi da aka gani a wani yanayi mai kamanceceniya da baɗala da wata Akuya, lamarin da ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta.

Matashin, Shamsu Yakubu mai shekaru 24 da ke zaune a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta Kano, ya shiga hannu ne bayan ɓullar wani bidiyonsa a dandalan sada zumunta musamman TikTok yana tsotsar farjin wata Akuya.

A cikin bidiyon da wani yake ɗaukarsa wanda ya yaɗu sosai a soshiyal midiya, an hasko matashin a wannan yanayin mai kama da baɗala tare da Akuyar.

Sai dai yayin da yake amsa tambayoyin mahukunta, matashin ya yi iƙirarin aikata hakan da nufin neman suna domin samun ɗaukaka ta dandalin sada zumunta.

Wannan lamari da ya fusata mazauna yankin ya sanya suka yi yunƙurin ɗaukar mataki a hannunsu, amma aka yi sa’a wani jami’in Hisbah ya tari hanzarinsu kuma aka cafke shi.

A yayin shan titsiye, matashin ya musanta zargin da ake yi masa, yana rantsuwa da Allah cewa bai tsotsi Akuyar ba.

“Na rantse da Allah ban tsotsi Akuyar ba, bakina kawai na kai kusa da wurin,” a cewarsa.

Matashin ya kuma bayyana cewa wannan shi ne karon farko da ya aikata irin wannan lamari yana mai nadamar cewa ba zai ƙara ba.

Sai dai duk da ya musanta cewa ba ya ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ko kayan maye, Hukumar Hisbah ta umarci a yi masa gwajin ƙwaƙwalwa.

Da yake martani kan lamarin, Mataimakin Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminuddeen Abubakar, ya yi Allah wadai yana mai cewa wannan abun kunya ya saɓa wa tarbiyya da koyarwar addinin Islama

“Abun takaici ne mutum ɗan Musulmi ya faɗa wannan abun kunya domin neman suna,” in ji Sheikh Aminuddeen.

Haka kuma, ya ce za a kai Akuyar Asibitin Dabbobi domin duba lafiyarta.

Sheikh Aminuddeen ya gargaɗi masu ƙoƙarin neman suna da wallafe-wallafen hofi marasa kan gado.