✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake bikin kaddamar da Ronaldo a Al-Nassr

Nan da kowane lokaci Ronaldo zai bayyana a tsakiyar filin wasan kungiyar domin yin ido hudu da masoya

A halin yanzu masoyan kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da ke kasar Saudiyya sun yi cikar kwari a filin wasanta inda take gudanar da bikin kaddamar da sabon dan wasan domin yin tozali da shi.

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya da kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana a tsakiyar filin wasan kungiyar Al-Nassr ne domin kaddamar da shi a matsayin sabon dan wasa.

Ronaldo ya ba wa magoya bayan kungiyar tabbacin kayatar da su da kuma ba wa kungiyar gudummawa a Gasar Kwallon Kafa ta kasar Saudiyya.

Tun da farko said da Ronaldo da manajansa da jami’an kungiyar Al-Nassr suka kammala jawabi da manema labarai.

Bayan nan dan wasan ya shiga dakin shirin ’yan wasan kungiyar inda ya gana da sabbin takwarorinsa.

Ya bayyana cewa kafin zuwans Al-Nassr, kungiyar ta na burge shi, saboda yadda ’yan wasanta suka murza leda, da hakin kansu.

Ya kuma bayyana shirinsa na ba da gudummawa domin ganin kungiya ta yi nasara.

A karshen mako ne muka kawo rahoto cewa kungiyar Al-Nassr da Cristiano Ronaldo sun sanya hannu kan yarjejeniyar kasancewarsa a kungiyar na tsawon shekaru.