Kabilar Bwatiye dai sun kasu kashi biyu ne akwai wadanda suke Jihar Adamawa zuwa Kamaru, sannan akwai wadanda suke yankin Bachama da Batak a Jihar Taraba.
A da ana ce da su Bwata da Bachama, su ne kuma ake ce da su Bwatiye. Malam Job Agai Sama, Sakataren Jam’iyyar PDP a Jihar Adamawa ya bayyana wa Aminiya yadda ake neman aure a kabilar Bwatiye.
Malam Job Agai Sama ya ce kafin dan kabilar ya ga macen da yake so ya aura, akwai wurare da dama da ake haduwa da su.
Daga cikin wuraren akwai wuraren bukukuwar gargajiya da suke yi kamar bukukuwan kamun kifi da aka fi sani da ‘Bware’ ko kokuwa wadda aka fi sani da ‘Fari’ da bikin biso ‘Tutula’ akwai kuma taron babbar majalisa da coci suke yi na zamani wadanda za a iya haduwa a daya daga mazaunansu kamar Fufore da Numan da sauransu.
Ya ce jama’a da dama suna haduwa a nan, kuma akasari a nan ne ake samun matan aure.
Ya ce bayan mutum ya samu wadda yake so, zai iya fada wa abokinsa ya yi maka iso idan za ka iya tunkararta kuma sai ka same ta ka fada mata abin da ke ranka na son aurenta.
Ya ce idan budurwar ta amince, sai ka fara zuwa gidansu, idan ba ka je ba to ba al’ada ba ce.
“Zuwa gidansu na tabbatar wa yarinyar cewa aurenta za ka yi sannan makwabta ma za su san cewa kana nemanta,” inji shi.
Ya ce, daga nan sai ya saurayi ya fada wa iyayensa cewa ya samu matar da zai aura. A nan mahaifin zai tambaya ko ’yar wane ne da asalinta.
Sannan za a bincika ko suna da mayu a danginsu ko babu. Idan an dace cewa zuriyarta masu jarumta ne, mahaifin zai yi na’am da haka.
Malam Job ya kara da cewa, bayan nan sai a nemi mutumin kirki tsayayye wanda ake darajawa da wadansu a dangi sai a tafi gidan su yarinyar, a samu mahaifinta sa nemi aurenta.
Ya ce bayan mahaifin ya fahimci tarihin yaro ko su ma suna da maita ko babu ko manoma ne masu jarumta a nan mahaifin yarinyar zai ce su je su sake dawowa.
Malam Job Agai ya ce idan suka sake komawa sai a ce su zo da shaidar cewa suna son aure yarinyar wato kayan baiko ke nan, kamar su farin kyalle da tunkiya da kudi daidai karfin mutum.
Ya ce tunkiyar da za a kai budurwar tunkiya ce wadda ba ta taba haihuwa ba da farin kyalle allamar an bude kofa ke nan da kuma tukwicin kudi. Wannan su ne shedar an yi mata baiko da dan wane.
“A wannan lokacin duk wadanda suke nemanta za su yi gefe, sannan a shirya yadda za a biya dukiya wato sadaki ke nan.
“Ranar da za a biya dukiya, dattijon da ya je tambaya da farko shi ne zai sake komawa da abokan ango. Ita kuma budurwa za ta sanar da kawayenta su shirya su shaida a kan dukiyar,” inji shi.
Ya ce tun zuwan farkon ake daidaitawa a kan nawa ne za a biya a matsayin dukiyar aure.
“Idan aka kawo dukiya misali daga Naira dubu 10 zuwa dubu 50. Bayan haka za a sake komawa sai a ba da dan lokaci sannan a ce an gama shiri domin sanar da dangin amarya ranar da za a dauko ta. Daga nan za a tsayar da rana tsakanin dangin miji da na amarya.
“Ranar da za a dauki auren, an shirya wa amarya abubuwan da za ta kai gidan wadanda a gargajiyance, ya kamata a sa mata tukunya mai kafa uku da daurarriyar tsintsiya da gatari da fartanya da kujerun gargajiya da za a daure sai a dora wa angon a kansa sannan sai a samu tunkiya ko saniya wadda dai za a zubar da jini (a yanka) domin amarya ta samu naman miya daidai karfin aljihunsu,” inji shi.
Ya ce, “Idan saniya ce akwai mai rike igiyar saniyar, za a kawo dawa da masara da garinsu da za a zuba su a su kwarya da tukwane, ana waka ana guda. Zuriyar amarya za su gargade ta kan ta yi ladabi da biyayya ban da bata musu suna da sauransu.
“Sannan sai a ba ta tukunya mai kafa ukun nan wadda ake kira da “Duwan Gwara.” Sai su ce da ita sun san ita ’yar gidan mutunci ce. Idan wani ya miki sharrin rashin tarbiyya wannan tukunyar ce za ta je da shi a mata adalci. Za a sa ta dauki tukunyar mai kafa uku da sassafe ta je kogi ta debo ruwa.”
Ya ce a cikin kayan da ango zai dauka akwai ciyawa wadda za a daure domin babu fitila. Sai a dauki ciyawar bukkarta daya sai tsoho a unguwar ya zo ya zauna ya kyatta ashana a karkashin jiyawar. Idan ba ta yi laifi ba za a ga ruwan ya tafasa da wuri.
“Za a bar saniyar da gatarin a waje, za a shigar da dawa cikin gida sai a bar garin tuwon a wajen. A nan ne abokan ango za su zo su biya kudi na al’ada kamar tukwici na Naira dubu daya domin bari a shiga da sauran kayan ciki. Sai an biya igiyar da aka riko saniyar kafin a yanka saniyar domin amaryar ta yi girki da naman,” inji Malam Job.
Ya kara da cewa, “Da sassafe abokan ango za su dauko amarya kuma sai an biya kudi kafin ta fito, kawayenta sai su yi ta guda.”
Ya ce a al’adar Bwatiye a kwarya ake sanya abinci masu zane mai kyau a jikinsu. Da misalin karfe 5:00 na safe tuwon amarya ya yi, sai a zuba wa dangi da tsofaffi.
Duk za a bi gidajensu a rabar da abincin. Sai a yi giya wadda za a kai wa tsofaffi, dole a kai wa uban ango giya da tuwo, nan ne za a gano cewa amarya ta iso. Daga nan sai a yi ta kade-kade da sauransu.
Malam Job ya ce akan yi rumfa inda amarya da kawayenta za su yi rawa da abokan ango har gari ya waye. Idan gari ya waye sai ta dauko kyalle ta sa wa ango a wuya sai a yi musu tafi, an gama auren ke nan.