✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka yi wa matashin dan kasuwa kisan gilla

Wasu da ba a sani ba sun yi gunduwa-gunduwa da sassan jikin matashin dan kasuwa mai kamfanin baburan haya na Gokada da ke Legas Fahim…

Wasu da ba a sani ba sun yi gunduwa-gunduwa da sassan jikin matashin dan kasuwa mai kamfanin baburan haya na Gokada da ke Legas Fahim Saleh.

An tsince gawar matashin mai shekaru 33 ne a ranar Talata a gidansa da ke Manhattan a Kasar Amurka kamar yadda jaridar New York Times habarto.

Ana zargi ‘yan ina da kisa ne suka kashe masanin kimiyyar kwamfutar da suka yi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsa da zarto mai aiki da lantarki.

An gano gawar Fahim Saleh ne bayan ‘yar uwarsa ta ziyarci gidan domin ta duba shi saboda ba ta yi duriyarsa ba.

‘Yan sandan sun ce wanda ya yi kisan ya yi kokarin bata alamun da za su taimaka wa masu bincike su gano shi, amma sun iske zarton da aka yayyanka sassan jikin mamacin a yashe.

Masu binciken sun ce sun samu zarton a jone a jikin lantarki, abin da ya sa su zargin zuwan ‘yar uwar Fahim ne ne ya sa makashin barin gidan cikin hanzari.

Bidiyon da na’urar nadar hoton sirri a cikin gidan ya dauka ya nuna lokacin da Fahim Saleh ke tafe wani mutum da ya rufe fuskarsa yana biye da shi a baya.

Bayan saukar marigayin daga matakala ya shiga cikin gidan ne sai mutumin ya cakume shi ta baya da kokawa.

Marigayi Fahim Saleh haifaffen kasar Saudiyya ne amma dan asalin kasar Bangaladesh kuma mazaunin Amurka.

Shi ne ya kirkiri kamfanin hayar babur na Gokada a Legas a shekarar 2018.

Ana ganin tsarin sufurin Gokada ya taimaka wa jama’ar Legas wajen kauce wa cinkoson ababen hawa tare da samar da aikin yi ga dimbin matasa.

Kamfanin ya tara Dalar Amurka miliyan biyar da dubu dari uku a shekarar 2019.