Kungiyar Lauyoyi Mata (FIDA) ta gudanar da tattaki a Jihar Kano don wayar da kai da nuna kyama ga irin cin zarafin mata da ake yi.
An gudanar da tattakin ne a ranar Talata, karkashin jagorancin shugabarta kungiyar, Barista Bilkisu Ibrahim Sulaiman, inda ta ce sun fito gangamin ne don nuna goyon baya ga ’yan uwansu mata kan yadda ake keta musu haddi.
- DAGA LARABA: Yadda Masu Kwacen Waya Ke cin Karensu Babu Babbaka A Kano
- A shirye muke mu mika Abba Kyari ga Amurka idan bukatar haka ta taso — Malami
Daruruwan mata dauke da kwalaye da rubutu a jikinsu, sun fara tattakin ne daga Sakatariyar Audu Bako zuwa kofar Gidan Gwamnatin Jihar Kano.
Yayin tattakin, mambobin kungiyar sun nuna damuwa game da yadda ake samun karuwar cin zarafin mata musamman ta hanyar yi musu fyade.
Kazalika, sun bayyana damuwa game da matsalar fyade da kuma yadda ake sace mata da kananan yara, musamman a yankin Arewacin Najeriya.
A baya-bayan nan satar kananan yara ta yi kamari a Jihar Kano, lamarin da ya jefa iyaye da dama cikin shakku da damuwa game da rayuwar ’ya’yansu kanana.
Ana ci gaba da samun karuwar matan da ake cin zarafinsu ta hanyar lalata da su da kuma wasu nau’o’in cin zarafi a sassa daban-daban na duniya.
Kusan a kowacce rana dai sai an samu labari cewa an yi wa wata ko wani fyade a Najeriya.
Har wa yau, kungiyoyi masu fafutikar kare hakkin mata da kananan yara, na ta gwagwarmayar jan hankalin gwamnatocin Najeriya kan kafa dokar ta-baci a kan masu yi wa mata fyade.