An yi jana’izar ƙarin sojojin Jamhuriyar Nijar 12 da ’yan ta’adda suka kashe a wata musayar wuta a Jihar Tillaberi da ke Yammacin ƙasar.
Gwamnatin sojin Nijar ta sanar ranar Talata cewa sojojin sun kwanta dama ne bayan sun kai ɗauki a yankin Anzourou inda suka ragargaza maharan da ake kyautata zaton masu iƙirarin jihadi ne.
- DAGA LARABA: Mun fi son mulkin sojoji —Al’ummar Nijar
- Na miƙa wa Tinubu saƙon sojojin Nijar —Abdulsalami
An gudanar da jana’izar dakarun bisa tsarin addinin Islama, wanda gwamnan jihar, Laftanar-Kanar Maina Boucar, ya halarta.
Harin na ranar Lahadi shi ne na baya-bayan nan da mayaƙa masu iƙirarin jihadi suka kashe sojoji masu yawa a cikin mako hudu da sojoji ƙasar suka yi juyin mulki.
A ranar 15 ga watan Agusta mahara sun kashe sojoji 17, suka jikkata wasu 20 a wani ɗauki-ba-daɗi a jihar ta Tillaberi, inda sojojin suka kashe ’yan ta’adda sama da 100.
A ranar 26 ga watan Yuli sojojin Nijar sun yi wa shugaban ƙasar Mohamed Bazoum juyin mulki kan dalilan da suka haɗa da rashin tsaro da gaza murƙushe mayaka masu iƙirarin jihadi.
Nijar da ma sauran maƙwabtanta a Yankin Sahel na fama da matsalar tsaro da hare-haren masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da ƙungiyoyin Al-Qaeda da IS.
Wannan matsala da ta yi wa yankin katutu na akalla shekaru 10 ta fara fantsama ne daga yankin Arewacin ƙasar Mali a shekarar 2012, inda ta shiga Burkina Faso da Nijar a 2015.