Dubban al’ummar Musulmi sun halarci sallar jana’izar fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Musa Ibrahim Albani Kuri, wanda ’yan fashi suka kashe a gidansa.
Da azahar din ranar Laraba aka yi jana’izar Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri a Masallacin Juma’a na kungiyar Izala da ke Bolari a garin Gombe.
A lokacin da ya halarci jana’izar, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya yi alkawarin “kamowa da hukunta wadanda suka yi wannan aika-aika domin ya zama darasi ga masu shirin yin haka a nan gaba.
“Sannan za mu fatattaki masu aikata miyagun laifuka daga duk sassan jihar nan, ” in ji gawmnan wanda ya ce kisan Sheikh Albani Kuri a gidansa ya girgiza bangaren tsaron jihar da a baya take zaune cikin aminci.
A cewarsa, hakan ya nuna muhimmancin gwamnati da al’ummar jihar su kara farga tare da daukar matakan da suka dace game sha’anin tsaro.
A safiyar ranar Sakataren Kungiyar Izala na Kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya sanar da rasuwar Sheikh Albani Kuri a hannun ’yan fashin da suka kutsa gidansa da ke unguwar Tabra a garin Gombe.
A ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Ibrahim Musa da kungiyar Izala, gwamnan Inuwa ya bayyana malamin a matsayin kogin ilimi da ke hada kan al’umma ba tare da nuna bambanci ba, “wanda kuma koyarwarsa ta amfani al’ummar Musulumi.”
Rasuwar malamin, a cewarsa, ta samar da gibi mai wuyar cikewa, kuma za a jima ana kewarsa.
A karshe ya lashi takobin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi jihar, ta hanyar bullo da sabbin dabaru da kuma daukar matakan da suka dace a kan kari.