✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kurakurai 8 na masu juyin mulkin Nijar

Daga Ɗanjuma Katsina 1. Kuskuren farko shi ne juyin mulkin da soja suka yi wa gwamnatin da jama’a suka zaba, kuma juyin mulkin na cin…

Daga Ɗanjuma Katsina

1. Kuskuren farko shi ne juyin mulkin da soja suka yi wa gwamnatin da jama’a suka zaba, kuma juyin mulkin na cin amana. Domin kuwa wanda aka amince masa ya amshi gwamnatin saboda kwadayin mulki.

Nijar kasa ce mai arziki, mutanen ta masu gaskiya ne, kuma jajirtattu ne, amma daya daga cikin abin da ya hana kasar cigaba da bunkasa akwai yawan juyin mulki.

2. Kuskure na biyu shi ne, daga tutar Rasha da masu juyin mulkin suka yi. Da masu juyin mulkin ba su danganta kansu da kowace kasa ba, sukan fifita kishin kasarsu sama da kowace kasa.

An maka ECOWAS a kotu kan shirin yaki a Nijar

ECOWAS ta sake kakaba wa Nijar sabon takunkumi

3. Kuskure na uku shi ne, muryar da aka ji shugaban sojan haya na Wagner yana goyon bayan juyin mulkin, kuma sojan da suka yi juyin mulkin ba su barranta kansu da muryar ba.

4. Kuskuren kin sauraren tawagar da gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta tura, suka hana su shiga kasar, suka killace su a bakin filin jirgin kasar. Kamata ya yi masu juyin mulki su bude kafofin tattaunawa ta ko’ina, su tura wakilai kasashen makwabta da na duniya su yi bayanin abin da ya kai su ga juyin mulkin.

5. Kulle sararin samaniyar kasarsu, wanda wata babbar hanyar zirga-zirga ce ta jiragen kasashen duniya. Jiragen yaki da na fasinja sun sha bamban. Mali, Burkina Faso da Guinea suna goyon bayan juyin mulkin, amma sararin samaniyarsu a bude yake, me ya sa Nijar za ta rufe nata?

6. Na shida gayyatar sojan hayar kasar Rasha na Wagna a kasarsu don su taimaka masu. Sojan Wagna ana masu daukar ‘yan ta’adda a Yammacin Turai. Don haka gayyatar su kamar fito-na-fito ne kai tsaye da Yammacin Duniya.

7, Na bakwai shi ne, amincewa da wata hadakar soja tsakaninsu da kasashen Mali da Barkina Faso. Wannan zai zama wani karin kalubale ga Yammacin Turai da ECOWAS, wanda sai sun ga abin da zai ture wa buzu nadi.

8. Na takwas shi ne, hana Wakilin Majalisar Dinkin Duniya da na kasashen Afrika da na ECOWAS damar shiga kasar. Wannan ya nuna sun kulle duk wata kofar magana. Sun ki su saurara, ya za a saurare su?

Makwabciyarmu kasar Nijar na cikin halin tsaka mai wuya, wanda matsalarta za ta iya shafar Afrika baki daya, amma kasar Nijar ce za ta fi tagayyara.

Ko da ECOWAS ba ta kai hari ba, in dai ba sulhuntawa aka yi ba, Yammacin Turai ba za su taba bari kasar ta zauna lafiya ba, in dai kasar na samun goyon bayan kasar Rasha da sojan Wagna, Mali da Barkina Faso a cikin ta.

Wannan wani halin gaba kura baya siyaki, kuma mugun tsaka mai wuya kasar take a ciki.

Ko sojan da suka amshi kasar za su bari kasar ta zama wajen gwada karfin Turawan Yamma da na Gabashi? Ko tattaunawa da sulhu da hangen nesa za su yi aiki? Wannan lokaci ne zai tabbatar.

Muhammad Danjuma Katsina, Dan jarida ne, mawallafin jaridun Katsina City News da jaridar Taskar Labarai da ke bisa yanar gizo