✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka tsige Shugaban Majalisar Dokokin Filato

Lalong ya musanta cewa yana da hannu a tsige Shugaban Majalisar daga kujerarsa.

A safiyar ranar Alhamis din da ta gabata ce, ’yan Majalisar Dokokin Jihar Filato, suka tsige Shugaban Majalisar, Honarabul  Nuhu Abok Ayuba da ke wakiltar mazabar Jos ta Gabas.

’Yan Majalisar bayan tsige Honarabul Nuhu, sun kuma maye gurbinsa da Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pingana ta Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar.

Mambobi 16 daga cikin 24 na majalisar ne suka kada kuri’ar amincewa da tsige shi a zaman majalisar cikin tsaro mai tsauri wanda Mataimakin Shugaban Majalisar, Saleh Yipmong ya jagoranta

Da yake bayani kan lamarin, Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Honarabul Daniel Naanlong, ya bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne domin su magance murkushe dimokuradiyya da karya ka’idojin majalisar da Honarabul Ayuba ke yi.

A cewarsa, Honarabul Ayuba bai cancanci ci gaba da jan akalar jagoranci a majalisar ba saboda aikata almundahanar kudaden da yake yi.

Ya ce tsohon Shugaban Majalisar, shi kadai yake tafiyar da harkokin majalisar, ba tare da tafiya da kowa daga cikin sauran shugabannin majalisar ba.

Ya ce Gwamna Simon Bako Lalong  na Jihar ya yi yunkurin gabatar wa Majalisar Kasafin Kudin Jihar na badi har sau uku, amma tsohon Shugaban Majalisar  yaki  ba shi damar yin haka ta hanyar rufe majalisar.

“Mun bi ka’ida wajen tsige tsohon Shugaban Majalisar, domin mun sami goyon baya na mafi rinjayen adadin ’yan majalisar da kudin tsarin mulki ya bamu na tsige shi.

“’Yan majalisar 16 cikin 24 da muke da su sun sanya hannu,  don haka mun sami kashi biyu bisa uka na ’yan majalisar da suka amince da shi.

“Kuma nan take muka zabi Yakubu Sanda dan majalisar mai wakiltar mazabar Pengana, a matsayin sabon shugaban majalisar.’’

Ba a bi ka’ida ba wajen tsige ni — Ayuba Abok

To amma da yake bayani kan yadda aka tsige shi, a wajen wani taron ’yan jarida da wata Kungiyar matasa, mai suna “Not Too Young To Run Movement’’ ta kira a Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata, tsohon Shugaban Majalisar Honarabul Ayuba Nuhu Abok, ya yi zargin cewa Gwamnan Jihar Simon Lalong ne, ya kitsa wannan tsigewa da aka yi masa.

Ya ce a matsayin Gwamna Lalong na tsohon Lauya kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, ya kamata ya san abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya kunsa.

“Abin da ya faru a Filato kan wannan al’amari, wani abin takaici ne,  inda tsohon Lauya kuma Shugaban Kungiyar gwamnonin Arewa, zai aikata wannan abu na rashin biyayya ga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

“Ya kamata ya bi abin da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ce, na sai an sami ’yan majalisa 16 a cikin ’yan Majalisar Dokokin Filato 24 da muke da su da suka amince a tsigeni, kafin a tsigeni’’.

Tsohon shugaban ya yi bayanin cewa, shi bai taba tilastawa kansa wajen yin aiki da gwamnan ba, domin shi a cewarsa yana yi wa al’ummar Filato aiki ne.

Ya ce, “mu wakilan al’ummmar Filato ne a majalisar, don haka duk abin da al’ummar Filato suka ce suna so shi ne muke yi a majalisar, amma gwamnan yana rusa wannan tsari.

“Abin da ya faru kan wannan lamari, gwamna ne ya tara wasu ‘yan majalisar guda bakwai, ya dauke su ya kai su zauren majalisar da misalin karfe 5 na safe, suka ce wai sun tsige ni, ba tare da bin ka’ida ba.

“Wannan tsamin dangartaka da ke tsakanina da gwamnan ta faro ne tun a kwanakin baya, lokacin da aka sami rikice-rikice a jihar nan, wanda muka nemi ya fito muka ya yi wa kowa adalci a Jihar nan.

“Tun daga nan ya ce sai ya tsigeni daga shugabancin majalisar, saboda haka ya zo ya yi amfani da jami’an tsaro, wajen aikata wannan haramtatcen al’amari.

“Don haka bamu amince da shi ba, domin mun san doka, kuma muna biyayya ga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

“Muna aiki ne da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, bamu taba sabawa Kundin Tsarin Mulkin kasar ba, kuma za mu ci gaba da yi masa biyayya.”

Ba ni da hannu a tsige Honarabul Ayuba — Lalong

A nasa bangaren, Gwamna Simon Lalong ya musanta cewa yana da hannu wajen tsige Honarabul Nuhu Abok Ayuba daga kujerarsa.

Gwamnan ya musanta wannan zargi da ake yi masa ne a wajen taron addu’a na shekara-shekara a Cocin Pentecostal Fellowship ta Najeriya da aka gudanar a ranar asabar da ta gabata a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Gwamnan ya ce Majalisar Dokokin Jihar tana zaman kanta ne, don haka tana da ’yancin gudanar da al’amuranta, ba tare da sanya bakin wani ba.

“Idan ba a manta ba, ni ne gwamna na farko a Najeriya da ya fara sanya hannu a dokar baiwa Majalisar Dokokin Jiha ’yanci cin gashin-kai a Najeriya, kuma na gabatar da wannan doka.

“Na yi haka ne saboda ina son na ga an tabbatar da dimokuradiyya a tsarin Majalisar Dokokin Jihohi.

“Na yi Shugaban Majalisa kuma an tsigeni a lokacin da nake kan wannan mukami, don haka bani da hannu kan tafiyar da harkokin majalisar balle kuma a ce maganar Shugabancin majalisa.

“Suna aikinsu ne bisa abin da suka zartarwa kansu da kuma dokokin kasa,’’ a cewar Gwamnan.

Shi dai tsohon Shugaban majalisar, Honarabul Nuhu Abok Ayuba wanda ke wakiltar mazabar Jos ta gabas, a wannan karo ne aka zabe shi, wato  zuwansa majalisar dokokin ta jihar Filato na farko ke nan.

Kuma bayanai sun nuna cewa, gwamna Lalong ya yi iyakar kokarinsa wajen ganin ya zama shugaban majalisar dokokin.

Rikici  tsakanin gwamna Lalong  da tsohon shugaban majalisar ya fara tasowa ne a lokacin da aka kai wani  hari a kauyen Yelwan Zangam, da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a kwanakin baya,  inda aka kashe mutane 37.

Bayan kai wannan hari ne Majalisar Dokokin Jihar ta bai wa gwamnan wa’adin makonni biyu ya shawo kan rikice-rikicen da ake yi a  Jihar ko ta tsige shi.

To amma wata majiya ta bayyana cewa, an fara samun sabani tsakanin gwamnan da tsohon Shugaban Majalisar ne tun a lokacin da aka yi zaben Shugaban Majalisar Matasan Jihar Filato.

Tun a nan ne aka yi zargin gwamnan ya yi watsi da dan takarar da ya fito daga bangaren tsohon Shugaban Majalisar, inda ya mara baya ga dan takarar da ya fito daga bangaren Kwamishinar Harkokin mata ta Jihar, Rebecca Adar Sambo.

Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa wannan abu da ya faru, ya bata wa tsohon Shugaban Majalisar rai sosai.

Wani Lauya mai zaman kansa da ke zaune a garin Jos kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Barista Lawal Ishak ya shaida wa wakilinmu cewa, wannan sauyi da aka samu na Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Filato ya yi dai dai.

Ya  ce a tsarin mulkin kasar nan, Shugaban Majalisa shi ne na uku a jiha, wato daga gwamna da mataimakinsa, sai Shugaban Majalisa.

“Shi shugaba a kowanne lokaci ana son ya kasance mai hangen nesa da hada kan al’umma, don tabbatar da zaman lafiya.

“To shi wannan tsohon Shugaban Majalisa da aka tsige, kwanakin baya da aka sami rikicin addini da kabilanci a jihar nan, ya fito ya yi wasu maganganu da basu nuna cewa shi shugaba bane.

“A cikin maganganganun da ya yi, ya ce wasu al’umma su dauki makami, su kare kansu wanda da dama wasu basu ji dadin wadannan maganganu da ya yi ba.

“Kuma a lokacin ya yi hira da Tashar Talbijin ta Channels, inda  ya yi  maganganu marasa dadi ga gwamnan jihar nan.

“Wadannan abubuwa basu dace da shugaba ba, domin shi mulkin dimokuradiya ana haduwa ne da bangaren zartarwa da bangaren masu dokoki da kuma bangaren shari’a, domin a ga an sami zaman lafiya.

“Don haka wannan mataki da aka dauka ya yi kyau. Kuma wannan mataki zai kawo cigaban al’ummar jihar Filato.”