A ranar Larabar makon jiya ’yan bindiga da aka kiyasta sun kai 20, suka kai hari Unguwar Joka a kauyen Tungan-Maje kusa da garin Zuba a Abuja, inda suka sace mutum 11.
Bayanai sun ce maharan sun shafe sa’a biyu a unguwar da ke gefen gari kuma kusa da gonaki da bishiyoyi, inda suka kutsa cikin wasu gidaje da suke ganin suna da wadata a kauyen, bayan tsallakawa ta katanga, tare da balle kofa ko tagogin gidajen.
Maharan sun kuma balle wani shagon kayan masarufi tare da kwashe kayan ciki suka dora a kan wadansu daga cikin mutanen da suka sace.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 1 a wurin shakatawa
- Boko Haram: Manoma miliyan 1 ba sa iya fita gona a Borno
Aminiya ta samu cewa maharan sun fice daga garin da misalin karfe 2:00 na dare bayan sun ji harbin bindiga daga ’yan sanda ciki da masu yaki da fashi da makami (SARS), da suka kai dauki yankin daga ofishinsu na Zuba bayan sanar da su.
Wata mai suna Grace Usas da maharan suka dauke tare da ’ya’yanta uku, ta ce bayan tafiya kamar ta sa’a daya a dajin Shenagu, sun yada zango a wani waje inda suka saki mutum biyar da suka hada da ita da ’ya’yanta biyu kanana .
Ta ce sauran wadanda aka sacen sun hada da wata mai ciki da wani dattijo, sai danta mai shekara 13.
“Wadansu daga cikin maharan sun tsaya a kanmu na wani lokaci, sannan suka wuce da mutum biyar da suka hada da ’yan mata uku masu suna Maryam Muktar mai shekara 17 da Onyinyechi Eze mai shekara 16 da Patience James mai shekara 13, sai kuma maza uku; Faruk Salisu mai shekara 11 da Daniel Usas mai shekara 14 da David Ajibola mai shekara 50.”
“Daga baya maharan sun umarce mu da mu koma kauyen namu, sannan suka tafi da mutum shida don ci gaba da garkuwa da su,” inji Misis Grace.
“A hanyarmu ta komawa gida ne muka hadu da ’yan sanda da ’yan banga a cikin dajin bayan kula da hasken fitilun da suke riqe da su, inda muka karasa zuwa kauyen tare.
Wani jagoran ’yan banga a garin, Yunusa Zakari Akoshi, ya shaida wa Aminiya a Laraba cewa, suna shirin fita neman maharan a ranar Litinin da dare, sai bayani ya zo musu cewa an sako mutum shida da suka rage, da misalin karfe 12:00 na dare a wani waje da ke kusa da kauyen Anagada.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa kowane iyali na mutum shida da aka sace, ya ba da Naira dubu 500, inda aka tara Naira miliyan uku aka kai wa masu garkuwar.
Ya ce “masu garkuwar sun karbe sabon babur daga hannun wanda ya kai musu kudin fansar da wayarsa, sannan suka sanar da shi cewa ya koma ta bakin hanya zai ga mutanen da ya zo karba.”
“Bayan nan ne kuma sai masu garkuwar suka kira wayar wadanda suka yi ta tattaunawa a kan abin da za a bayar, tare da shaida musu cewa yaransu na waje kaza, to a can ne aka je a ka dauko su da mota da misalin karfe 12:00 na dare, sannan wanda ya je biyan kudin ya dawo gida bayan wani lokaci,” inji majiyar.