Farashin tikicin jirgin sama zuwa wasu yankunan Arewacin Najeriya ya karu da fiye da kashi 100 bayan dakatar da kamfanin Azman Air.
Sakamakon dakatar da Azman, tikicin jirgin da ake siya N35,000 daga Legas zuwa Kano ba dawowa ya yi tashin gwauron zabo zuwa N56,000 a jirgin Max Air, Air Peace kuma N73,000.
- Gwamnatin Kano za ta gurfanar da mawakin yabo, Bashir Dandago
- Yadda mutanen Jingir suka yi wa ’yan bindiga kofar rago
- Bayan kai masa hari, Gwamna Ortom ya ziyarci Buhari
- Mutumin da yake sayar wa da ’yan bindiga babura ya shiga hannu a Kano
A lokacin da Aminiya ta bincika, har an riga an saye kujerun jiragen da ke Kano zuwa Legas na ranar Talata.
Hakan ta sa fasinjoji matsa wa ejen-ejen da tambaya don neman sanin yaushe kamfanin Azman Air zai ci gaba da gudanar da harkokinsa.
Kafin dakatarwar da Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta yi wa Azman a makon jiya, kamfanin na yin sawu 15 a kullum, yawanci zuwa Kano, Kaduna, Maiduguri, Kebbi, Yola da sauransu a Arewacin Nejiya.
Bayan dakatarwar da aka yi wa Azman, sauran kamfanoni sun kara yawan sawun da jiragensu suke yi zuwa wuraren da Azman ya fi karfi.
Misali, bayan dakatar da Azman, kamfanin Max Air ya karo sabbin jirage biyu domin jigilar fasinja a wuraren da Azman ke jigilar fasinja.
Max Air ya kuma kara yawan zirga-zirgarsa daga Abuja zuwa Sokoto a koma Abuja; Abuja zuwa Katsina a koma Abuja, sannan Kano.
Ya kuma kara yawan sawun da yake yi daga Abuja zuwa Sakkwato a koma Abuja daga daya zuwa biyu, haka ma daga Abuja zuwa Kano da Maiduguri.
A ’yan kwananin da suka gabata kuma, kamfani Aero Contractors kuma ya fara jigilar fasinja daga Kano zuwa Abuja.
Aminiya ta kuma gano cewa halin yanzu, ana fama da karancin jirage a hanyoyin da Azman ya saba jigilar fasinja, kamar Kebbi da Gombe.
Wani ejen din tafiye-tafiye, Mista Benjamin Shotunde ya ce dakatar da kamfanin ya haifar da matsalar a harkar jigilar fasinja.
“Ba mu da isassun jirage a Kano, Kaduna har ma da Abuja. Da ma can lallabawa ake yi.
“Duk yadda aka rasa wani kamfani, ko da hanya daya kacal yake bi sai abin ya kwao matsala. Arik na fama da matsaloli, Air Peace kuma na da karancin jirage,” inji shi.
Wani mai sharhi a kan sufurin jiragen zama, Mista Olumide Ohunayo ya ce da ma akwai yiwuwa karuwar farashin tikicin jirgi sakamakon dakatar da Azman.
Ya ce duk da haka, kamata ya yi a bar hukumar da hakkin kula da hakan ya rataya a kanta ta dauki mataki.
A halin yanzu, Azman na shirye-shirye tare da kwarin gwiwar ci gaba da harkokinsa a wannan makon, bayan NCAA ta gama tantance kamfanin.
NCCA za ta sanar da matakinta a kan Azman daga rahoton da kwamitinsa na sa idonsa ya bayar bayan gudanar da bincike a kan kamfanin.
Azman ya sanar ta shafinsa na Twitter cewa akwai yiwuwtar fitar da jadawalin zirga-zirgar jiragensa daga ranar Laraba.