✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo.

Babban Hafsan Rundunar, Iya Mashal Hassan Abubakar, ne ya sanya sabbin matuƙa jiragen anini a yayin bikin da aka gudanar a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar (401 FTS) da ke Kaduna.

Yayen nasu ya zo ne watanni kaɗan bayan rundunar ta mallaki sabbin jiragen yaki guda 12, waɗanda suka ƙara mata ƙaimi wajen ayyukan samar da tsaro da kuma ta’addanci.

A wani taro da ya gudanar da tsofaffin sojojin rundunar a Kaduna, Iya Marshal Hassan Abubakar ya shaida musu cewa rundunar tana jiran karin jiragen yaƙi guda 34.

Ya buƙaci waɗanda aka yayen nasu da su yi amfani da wannan dama wajen cika burin ’yan Najeriya da ke da kyakkyawan fata a kansu.

Rundunar na da nufin amfani da sabbin matuƙan jiragen nata a ayyukanta na tabbatar da tsaro a sassan kasar nan.