Sojoji sun kama wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane ɗauke da tsabar kuɗi Naira miliyan 13 a kan hanyar Kaduna zuwa Jos a Jihar Kaduna.
Dakarun Rundunar Operation Safe Haven sun kuma ƙwace bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da harsasai 30 a hannun ɗan ta’addan a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna.
Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya ce dubun ɗan ta’addan ta cika ne a wani shingen bincike da ke yankin Agameti a kan babbar hanyar Wamba zuwa Jos.
Manjo Zhakom ya ce a ranar Laraba, sojoji suka tsayar da wata mota ƙirar Volkswagen Golf da ke ɗauke da mutum uku, amma kafin ta ƙaraso inda za ta tsaya, biyu daga cikin mutanen suka fice suka tsere.
- Sojoji sun kashe ’yan fashin daji masu yawan gaske a Zamfara
- Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa
Ya bayyana cewa sojojin sun gano ramin harbin bindiga da kuma jini a jikin motar, kuma direban ya yi yunƙurin ba su cin hanci amma suka ƙi karba.
“Suka kama shi, bayan cikar wanda ake zargin da kuma cikin motar suka gano bindigogi biyu ƙirar AK-47 da harsasai 30 da wayoyi guda uku da layu da tsabar kuɗi N13,742,000, da wuƙa da sauransu.
“A yayin bincike ya amsa cewa yana da hannu garkuwa da mutane a kan hanyar Jos zuwa Makurɗi, kuma ya amince ya kai sojoji maɓoyarsa.
“A yayin da suke tafiya, wanda ake zargin ya yi yunƙurin ƙwace makamin jami’anmu, amma suka murƙushe shi” in ji shi.
Manjo Zangon ya ce rundunar na ci gaba da zurfafa bincike domin kamo sauran ’yan ta’addan da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.