Al’umar Jihar Bauchi musamman mazauna Unguwar Kofar Wambai da ke cikin garin Bauchi sun shiga jimami da alhini sakamakon wani abin bakin ciki da ya faru, inda wani mutum da ba a san ko wane ne ba, ya yaudari wadansu almajirai biyu ya kira su a kan zai ba su abinci amma ya fasa kan daya daga cikinsu ya kwashe kwakwalwarsa ya tafi da ita.
Lamarin wanda ya tayar da hankali tare da firgita jama’a ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata a garin Bauchi.
- Najeriya na cikin kasashen da ake gallaza wa yara – UNICEF
- China za ta ‘kwace’ filin jirgin saman Uganda saboda bashin $207m
Yadda lamarin ya faru – Malami
Da yake zantawa da Aminiya, Alaramma Muhammadu Auwalu, wanda almajirinsa ne aka yi wa haka, ya ce ranar Asabar da ta gabata bayan sun yi karatun safe da yara, sai suka ce za su je su karya, su zo su tafi gona.
Da suka fita sai wanda aka kashe ya ce wa dan uwansa su je bakin hanya su sha iska su dawo.
Malam Auwalu ya ce sai dayan ya ce ba ka tuna abin da Malam ya ce ba ne cewa mu je mu karya mu dawo? Sai marigayin ya ce yanzu za su dawo.
“Da fitarsu ba a yi minti 30 ba sai dayan ya zo a guje cikin firgici yana cewa ana kashe shi! An kashe Yunusa!”
Sai muka ce wace magana ce wannan Aminu? Ganin jiknsa da jini, sai muka dauki babur muka bi shi a kidime. Bai ma gane wurin ba har muka gane wajen a kan wani dutse a bayan inda ake wanke babura. A gefe kuma ga yara suna kwallo.
“Lokacin da muka isa kansa, ya yunkura sau biyu sai ya kwanta bai sake motsi ba, ashe ya rasu. Innalillahi wa inna ilaihirraji’un!
“Da na ga haka sai na daga waya na kira mahaifinsa, wanda yake kasar Misau, ya ce mini yaya yara? Ba ku tashi daga makaranta ba ne?” Domin ya ji hayaniya, wadanda suke kwallon ma sun bari sun biyo mu. Ga dansa a kwance cikin jini, na ce masa an tashi, nan na yi masa bayani.”
Malamin ya kara da cewa “Kuma ba mu ga kowa a wajen ban da ’yan kwallon da suka biyo mu. Shi ne muka kira jami’an tsaro, suka nemo mota muka dauke shi zuwa ofishin ’yan sanda, daga can muka tafi asibiti, likita ya gwada ya ce ya cika.
Da likita ya tabbatar da rasuwarsa sai na kira mahaifinsa na fada masa.
Ya ce to, a yi masa jana’iza. Na ce masa za mu jira ya zo. Shi ne muka jira shi ya zo daga Misau muka yi masa Sallah.”
Ya ce, “Baturen ’yan sandan ya ce in mun kai mu dawo. Da muka zo ya yi mana ta’aziyya, sannan ya ce suna son su ji ko akwai wani korafi daga iyayen yaron. Sai mahaifin yaron ya ce ba ya da wani korafi, wannan abu daga Allah ne. Amma ba zai hana jami’an tsaro su bincika ko za su gano wadanda suka aikata wannan abu don a hukunta su ba.”
Malamin ya ce almajirin bai kai shekara daya da zuwa makarantar ba kuma karatunsa izu biyu ne.
‘Yadda aka yaudare mu aka kashe abokina’
Abokin tafiyar marigayin mai suna Aminu da abin ya faru da su, cikin kaduwa da rudewa yana kuka ya shaida wa jama’a cewa lokacin da mutumin ya gan su ya kira su ne a kan su je wani gida za a ba su abinci.
Da suka je sai ya kafe babur dinsa ya shake Yunusa ya kifar da shi ya kwada masa dutse a ka, sai jini ya fito. Shi ne shi ya samu ya gudu ya fada a gida.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi SP Muhammad Ahmad Wakil ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya ce yaran biyu mutumin ya kira daya sunansa Muhammad Yunusa mai shekara 11 da Aminu Yusuf mai shekara 12.
Ya ce da mutumin ya kira su cewa zai ba su abinci sai ya dauko dutse ya fasa kokon kan Yunusa ya cire kwanyarsa ya tafi da ita, kuma ba wanda ya gan shi.
Wakil ya ce da aka fada wa ’yan sanda sun je wajen suka samu Yunusa a kwance cikin jini, suka dauke shi suka kai shi asibiti inda likita ya ce ya rasu.
“Take Kwamishinan ’Yan sanda ya umarci Baturen ’Yan sandan Shiyya ta Daya (A Dibishan) cewa ya tabbatar ya kamo wanda ya aikata wannan mugun aiki don a gurfanar da shi a kotu.
Kwamishinan ya kuma bukaci iyaye da su kula da ’ya’yansu, kuma su gargade su cewa kada su ga mutumin da ba su san shi ba ya ce zai ba su wani abu su bi shi,” inji shi.
Ya ce ya kuma bukaci jama’a su taimaka musu da bayanan da za su taimaka a kama wadanda suka aikata wannan mugun aiki.
Shugaban Malaman Tsangaya na Jihar Bauchi, Alaramma Zakariya’u Daudawa ya ce ya kadu kan abin da ya faru, “Mun sanar da gwamnati kuma Gwamna ya turo kwanishina domin sake jajanta wa wadanda wannan al’amari ya shafa.
“Muna rokon Allah Ya gafarta wa wannan yaro kuma duk inda wadanda suka aikata wannan mugun aiki suke, Allah Ya sa a kama su kuma za mu yi addu’o’i na musamman don ganin Allah Ya tona asirin wadanda suka yi wannan mugun aiki,” inji shi.
Ya ce “Faruwar lamari ta sa dole za mu sake zama mu jawo hankalin ’yan uwa almajirai masu tsangaya don mu dauki matakan kariya ta yadda za su rika kiyaye wuraren da suke zuwa.