Wani dan bindiga ya harbi wata budurwa mai shekara 15 sau hudu a gaban mahaifiyarta a bainar jama’a.
Dan bindigar ya harbi yarinyar da ke ajin karshe a makarantar sakandare ne a yayin da ita da mahaifiyarta suke jiran babur din haya don komawa gida bayan tashi daga shagon mahaifiyarta.
- Bidiyon Dala karya ce tsagwaronta —Ganduje
- An kai wa Gwamnan Binuwai hari
- ’Yan bindigar Zamfara sun haramta hakar ma’adinai
“Ina da karamin kanti a NOVA a Basiri inda nake sayar da ’yan kayayyaki.
“Mun rufe shago, muna neman babur din haya mu koma gidanmu a Ifesowapo, Better life, sai ga wani mutun ya sauka a babur ya harbi ’yata,” inji mahaifiyar.
Ta ce mutumin da ke sanye ne da babbar riga, ya yi harbin ne a cikin mutane, kuma nan take mutane suka yi ta guje-gujen neman tsira.
A cewarsa, bayan tafiyar maharin a babur din da aka kawo shi ne ta lura cewa ’yarta na kwance jina-jina da harbi a kirjinta da cikinta da hannunta.
’Yan sanda sun baza komarsu don ganowa da kuma kama wanda ya harbi dalibar mai suna Ayomide Adaranijo.
Harbin da aka yi mata ya sa dalibar ta kasa kammala rajistar jarabawar kammala sakandare na WAEC da ake kan yi a halin yanzu.
A halin yanzu dalibar na kwance ana jinyar ta a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Ekiti (EKSUTH), da ke garin Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti.
Mahaifiyarta ta ce, wasu mazauna da aka yi harbin a kan idonsu ne suka taimaka aka kai yarinyar asibitin EKSUTH.
“Ma’aiktan lafiya sun yi kokari sosai, saboda na dauka ta mutu; Sun yi gaggawar cire harsashin daga cikinta, kirjinta da hannayenta.
“Kannenta sun tafi gida lokacin da abin ya faru, watakila da abin ya fi haka muni.
“Har yanzu ban san dalilin da ita kadai aka harba ba daga cikin kusan mutum takwas da ke wurin.
“Ba a shekara biyu da dawowata nan Ado Ekiti daga Ibadan, bayan rabuwarmu da mahaifinta, kuma ban da matsala da kowa. Har yanzu abin na daure min kai,’’ inji ta.
Ta ce, “’Yata ba mai yawan magana ba ce, balantana ta bata wa ani rai wurin magana. Ina roko a yi cikakken bincike a hukunta wanda aka samu da laifi,” inji ta.
Dattijuwar ta ce da kyar da taimakon jama’a suka hada N150,000 kafin aka yi wa yarinyar aiki, kuma sai kashe kusan Naira dubu dari biyar karin a sallame su kuma ba ta da halin su.