Masu sana’o’in hannu da ƙananan masana’antu a yankin Arewa sun shiga mawuyacin hali bayan ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki a yankin.
Iyalai da magidanta suna ɗanɗana kuɗarsu, a sakamakon wannan matsala wadda ta sa a wasu yankunan Arewa aka shafe kimanin kwana 10 babu wutar lantarki.
Yankin Arewa ya tsinci kansa a wannan hali ne a sakamakon lalacewar layin lantarki mai ƙarfin 330kV DC da ke isar da wutar zuwa yankin.
Wannan matsala ta faru ne a lokacin da ake fama da tsadar rayuwa, inda ake ci gaba da kokawa kan tashin gwauron zabon man fetur da na kayan masarufi a Nijeriya.
- Za mu bar Nijeriya idan ba a bari mun ƙara kuɗin kiran waya ba —MTN
- Gwamnonin PDP sun gana don warware matsalolin jam’iyyar
- DAGA LARABA: Shin Duka Ne Hanyar Ladabtar Da Yara Mafi Inganci?
Hakan ta tilasta wasu masu ƙanana da matsakaitan masana’antu a Arewa rufewa, a yayin da wasu ke lallabawa da ƙyar.
Kamfanoni casar shinkafa
Wani ɗan kasuwa mai matsakaicin kamfanin casar shinkafa a Kano, Bashir Ismail Usman, ya ce ɗauke wutar ta sa kamfanin ya dakatar da aiki saboda ba zai iya jure sayen man dizel ba.
Bashir ya ce rashin wutar ta sa ƙananan masana’antun casar shinkafa kimanin 50 daina aiki a cibiyar masana’antun shinkafa da ke Kwanar Dawaki.
Ya ce hatta manyan masana’antun ƙasar shinkafa suna ji a jikinsumda kuɗin sayen dizel a sakamakon ɗauke wutar.
Ya ɗora laifin tsadar shinkafa a kan yawan kuɗaɗen da kamfanonin suke kashewa wajen sayen man dizel.
Teloli da masu sana’ar hannu
A Jihar Jigawa inda aka shafe kwana 10 wutar lantarki, wani tela unguwar Sha’iskawa da ke garin Dutse, Yusha’u Isma’il, ya ce ya shafe kwana 10 rabon da ya yi aiki a shagonsa.
Ya ce rashin wutar da tsadar mai sin jefa shi cikin matsala inda kwastomomi suke ta addabar shi, duk da cewa suna sane da wannan matsala.
Shi ma wani tela a Kasuwar Dutse, Ibrahim Ahmad, ya ce yawancin teloli a kasuwar sun daina aiki saboda rashin wutar da tsadar mai.
Wani tela mai suna Muhammad Sani mai kamfanin ɗinki na Zazzau Designers Tailoring Services, ya ce rashin wutar da kuma tsadar mai sun shafi sana’arsa.
Ibrahim Isma’il tela ne a Gombe, inda ya bayyana cewa ya shafe mako guda yana bude shagonsa, amma kaya fiya biyar kawai ya ɗinka saboda rashin wuta.
Ya ce tsadar mai da rashin wutar sun sa shi da sauran teloli ba sa iya amfani da manyan kekunan ɗinki masu amfani da wuta.
Shi ma wani tela a cibiyar ’yan jarida da ke Gusau a Jihar Zamfara, Abdullah Musa, ya ce yawancin teloli a garin sun daina buɗe shago.
Ya ce yawancinsu masu ƙaramin ƙarfi ne da ba za su iya jure sayen janareta ko tsadar mai ma, sai wutar lantarki.
“Yanzu kuma wannan matsalar ta ƙara dagula harka,” in ji shi.
Masu sana’ar hannu
Wani mai sana’ar walda a Kano, Danladi Ibrahim, ya ce rashin wutar ta gurgunta sana’arsa, saboda tsadar mai.
Ya ce duk da cewa matsalar wutar lantarki a Arewa ba sabon abu ba ne, amma dole sai gwamnati ta yi abin da ya kamata, idan ba haka ba, talakwa ba za su daina shan wahala ba saboda matsalar wutar lantarki.
Ya ce, “sana’ar walda nake yi inda muke ƙera ƙofofi da sauransu, amma yanzu mun kasa yin komai saboda rashin wutar lantarki kuma mai yi tsada.
“Mu dai muna iya ce gwamnati ba ta da wani amfani a wurin sai dai wahalar da mu.”
Wata mai sayar da kayan sanyi a Gombe, Hajiya Tasalla ta ce yanzu ba ta iya samun ƙanƙara a sakamakon ɗauke wutar.
Ta ce, “yanzu a nan unguwar Fadama babu inda zan samu ƙanƙara sai na je Kowa Cost. To daga ina zan samu kuɗin mota. Dole sai dai in ƙara farashi, ga shi yanzu tsadar rayuwa ta sa ba fite sayen lemon kwalba na.”
Jamilu Abdulwahab mai shagon ‘Business Centre’ a daura da Babbar Kotun Tarayya da ke kan Titin Gyaɗi-Gyaɗi a Kano ya ce a baya bai fiye amfani da janareta ba, amma matsalar wutar tavsa yanzu wuni yake amfani da janareta.
“Idan na yi amfani da janareta, kuɗin mai zai cinye ribar, karshenta ma jarin ya karye,” in ji shi.
Wani mai sana’ar cajin waya a Kastina, Abba Dollar, ta ce rashin wutar ta zame musu kamar zuma kamar mafarki.
Masu shagon aski
Yusuf Yusuf Gummi mai shagon aski a garin Gusau, Jihar Zamfara ya ce ya sayo injin janareta saboda matsalar, amma duk da haka masu zuwa aiki suna ƙorafi kan tsadarsa.
Wani mai shagon aski a layin Paki Road a unguwar Tudun Wada a Jihar Kaduna, Jamilu Ibrahim ya ce sun koma amfani da makana mai riƙe caji.
Ya ce, “nakan yi cajin su da dare, amma yanzu rashin wutar nan ya ƙara dagula al’amura.”
Ya ce, “kafin in sayo janareta N20 nake askin yara, manya kuma N300, amma yanzu na yara ya koma N250, manya kuma N450 saboda tsadar mai. Amma duk da haka mutane suna ƙorafi cewa ya yi tsada a wannan yanayi na tsadar rayuwa.”
Wani mai shagon aski a Jihar Adamawa, Mista Babs Cuts, ua ce unguwar da yake a layin Band A suke kuma suna samun wuta yadda ya kamata, don haka bai damu da injin janareta ba.
Amma ya ce wannan matsa ta sa ya koma amfani da inji, wanda hakan kawo masa koma baya wajen samun kwastomomi saboda tsadar kuɗin mai.
Umar Faruk mai shagon aski na Decent Barbers a Kano, ya ce ya yanzu kwana uku a jere da yake amfani wutar lantarki mai amfani da hasken rana a shafin nasa.
Shi kuma Abdullahi Sani da ke aski a Kastina ya ce tsadar mai ta sa ba ya iya kunna inji a shagonsa.
Ya ce gidansu ya ke zuwa idan an kuna inji ya yi cajin makanarsa.
Amma ya ce duk da haka ya lura an samu raguwar masu zuwa aski a ’yan kwanakin nan.
Girman matsalar
Yankunan Arewa ta Yamma da Arewa ta Gabas da wani yanki na Arewa ta Tsakiya sun kasance a cikin duhu sakamakon lalacewar layin lantarkin mai ɗaukar megawat 160.
Lalacewar layin a ranar Lahadi ya shafi wutar da kamfanonin rarraba wutar lantarki na Kano da Kanduna da Jos.
Layin na 330kV DC, wanda ke ,,,,ya lalace ne bayan da aka koma kansa bayan lalacewar layuka biyu Shiri zuwa Kaduna wanda barayi suka lalata a ranar Juma’a.
A sakamakon haka, al’ummar jihohin da ke yankunan Arewa da abin ya shafa, sun yi aƙalla kwanaki uku babu wutar lantarki.
Wannan ƙari ne a kan rashin wutar lantarki da aka yi fama da ita a faɗin Najeriya, inda a makon da ya gabata kaɗai babban layin rarraba wutar a ƙasar ya ɗauke sau uku.
Sakamakon haka, wasu yankunan sun shafe kwanaki uku zuwa 10 babu wutar.
Daga ranar 4 ga watan Fabrairu zuwa yanzu, sau bakwai aka samu lalacewar babban layin wutar lantarki a kasar, mai yawan al’umma sama da miliyan 220.
Kamfanin Samar da Wutar Lantarki a Nijeriya (TCN) ya ce, duk da haka, kawo yanzu sau ɗaya ne wutar ta ɗauke gaba ɗaya a fadin ƙasar a bana.