Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce za ta hukunta masu yada hotunan sojojin da aka kashe a wurin yaki a shafukan zumunta.
Ta sanar da hakan ne cikin damuwa tare da kiran ’yan kasar da su daina yada hotunan a matsayin abin wasa a kafafen sada zumunta.
- ‘Jami’an gwamnati na wa jami’an tsaro manakisa a yaki da ta’addanci’
- Jama’ar gari sun hallaka mai garkuwa da mutane a Sakkwato
- An cafke Basarake da iyalansa kan zargin garkuwa da mutane
“Rundunar ba za ta lamunci wannan wulakanci da rashin kishin kasa ba, daga yanzu za mu dauki matakin doka don kare sojojin da suka rasu a fage yaki daga wulakanci a shafukan sada zumunta ko wani dandali.
“Mutum ya yi tunanin irin damuwa da radadin da iyalansu za su ji da ganin hotunan gawarwarkin masoyansu da ake yadawa kafafen sada zumunta,” inji sakon kiran da kakakin Rundunar, Birgediya Mohammed Yerima, ya fitar a ranar Talata a Abuja.
Yerima ya ce sojojin sun rasu ne a wurin gudanar da halastaccen aikinsu, saboda haka yada houtunan rashin kishi ne kuma abin zargi, wulakanta wadanda suka sadaukar da rayukansu ne wurin kare jama’a.
Ya ce, “Sojojin jarumari ne da suka sayar da rayukansu domin tsare jama’ar kasa domin ’yan Najeriya su samu aminci, saboda haka ba su dace da irin wannan wulakanci ba.”
Ya yi mamakin ribar da masu yada hotunan tare da mayar da sojojin da suka rasu ko suka samu rauni abin dariya, za su samu daga kafafen sada zumuntan.
“Ana yin wadannan ayyukan rashin kishin ne ba tare da lura da tunanin wadanda suka mutu ko danginsu ba.
“A wasu lokuta, ’yan uwansu ba su kai ga samun labarin rasuwar tasu ba, amma sai su yi rashin sa’ar cin karo irin wadannan hotuna masu matukar tayar da hankali.”