✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yabon Manzon Allah (S.A.W.)

A wannan wata ne na Rabi’ul Awwal ake bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu (saw). Fasihin sha’iri, Malam Nasiru ya rubuta wannan waka, tun a…

A wannan wata ne na Rabi’ul Awwal ake bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu (saw). Fasihin sha’iri, Malam Nasiru ya rubuta wannan waka, tun a ranar 26 ga Safar, 1411 BH (15 ga Satumba, 1990), domin yabon shi manzon, fiyayyen halitta.

Amshi: Manzo Rasulu muna yaba maka.
* * * *

1. Na gode wa mahaliccina,
Allahu mai girma da daukaka.

2. Sannan salati har taslimi,
Gunsa Rasulullahi mai Makka.

3. Yau shauki ne ya lullube ni,
Ya Sayyadi me zan fada maka?

4. Ba ni da kalmomi na yabon ka,
Sai dai salati zan ta yo maka.

5. Ya Rabbi salla ala Mukhtari,
Mazonka wanda ka bai wa daukaka.

6. Wato Muhammadu baban Kasim,
Wannan da ka bai wa kitabuka.

7. daha da ka bai wa cetonmu,
Babu kamarsa a anbiya’uka.

8. Shi ne ka bai tafki na Kausara,
Ranar kiyama Musdafa naka.

9. Wanda ka aiko wa da Buraka,
Domin ya je farfajiya taka.

10. Shi ne wanda ka yaye hijabi,
Ya je gare ka a can sama’uka.

11. Ka tattara masa dukka mukamai,
Wanda ka bai wa anbiya’uka.

12. Annabi Isa Ruhullahi,
Musa kuwa shi ne kalimuka.

13. Ka daukaka matsayin Idrisu,
Ibrahim shi ne Khaliluka.

14. Annabi Salihu ke da Taguwa,
Ka bai Sulaimanu riyahuka.

15. Annabi Yusifu ka bai kyawu,
Nuhu ko amsawar du’a’uka.

16. Amma Muhammadu Saifullahi,
Shi ne fiyayyensu Habibuka.

17. Ka daukaka shi zuwa ga muntaha,
Sannan kuma shi ne Khaliluka.

18. Kyawun Yusifu bai kai nasa,
Don daha yanki ne na nuruka.
19. Babban abin da ka bai wa Muhammad,
Shi ne na ceton mu a gu naka.

20. Lallai Muhammadu gun Allahu,
Dukka halitta ba kama taka.

21. Kai ne ka yo zance da Barewa,
Lallai babu kwatankwaci naka.

22. Har zaki ma shi da ja-ciki,
Sun gasgata ka suna yabo naka.

23. Hatta damo ya shaida batunka,
A gaban dukkannin sahabuka.

24. Farin wata ya zo shi gabanka,
Don nuna shaida kan batu naka.

25. Kai ne ruwa ya fito daga yatsun,
Hannunka Manzo daha mai Makka.

26. Ya shugaban dukkanmu halitta,
Duk anbiya sun jinjina Maka.

27. Tutar yabo hannunka za a sa,
Ranar kiyama ba kama taka.

28. Kai za ka fara shiga Aljanna,
Sai kuma dukkan masu bi naka.

29. kaunar ka Manzo ta shiga raina,
Kullum yawan shauki nake maka.

30. kimarka ba wani wanda ya san ta,
Sai dai kadan zai ambata maka.

31. Allahu wanda Ya yi ka hakika,
Shi ne Ya san kimar da yai maka.

32. Kai makiyi naka ya yi hasara,
A duniya har ma ga mai duka.

33. Ya lalace ya balbalce,
Tun da zagon kasa za ya yi maka.

34. Wallahi gara na kaunaci jaki,
Ko alade da na so maki naka.

35. Ai gara ma na zamo ni makaho,
In dai za na ga masu ki naka.

36. Allah Ka karya maki Muhammadu,
A ko’ina yake don isa taka.

37. Ya ’yan uwa ku mu begi Musdafa,
Dare da rana wajje ko daka.

38. Mui ta salati gun sa Ahmadu,
Sai ku ga mun sassamu daukaka.

39. In an fade shi mu rinka salati,
Sallallahu ala Nabiyyika.

40. Shi ne tafarkin samun khairi,
A duniya har ma da arzuka.

41. Mai son Annabi ba shi fargaba,
A duniya duk inda yaz zaka.

42. Balle ranar gobe kiyama,
Inda ake a’auna ayyuka.

43. Ranar ne zai samu mukamai,
Da martaba sannan da daukaka.
44. Allah dada mana kaunar Manzo,
Har lokacin rabuwa da rayuka.

45. Allah ka ba mu yawan yin hairi,
Babu riya domin Rasuluka.

46. Nan zan tsaya da kasidar tawa,
Manzo Rasulu muna yaba maka.

47. Ni ne Muhammadu Nasiru Garba,
dan Ahmad mai son ya je Makka.

48. Ni godiya ce ya Allahu,
Kullum a koyaushe nake maka.

49. Nai gaisuwa gunka ya Rasulu,
Har ma da Alaye Sahabuka.

50. Baitocin kuwa su Hamsin ne,
Na yo su don kauna da so naka.

ALHAMDU LILLAH