“Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ku yabi Allah a cikin haikalinSa, ku yabi karfinSa a sama, ku yabe Shi saboda manyan abubuwa wadanda Ya aikata, ku yabi mafificin girmanSa, ku yabe Shi da kakaki, ku yabe Shi da garaya da molaye, ku yabe Shi da bandiri kuna taka rawa, ku yabe Shi da garaya da sarewa, ku yabe Shi da kuge, ku yabe Shi da kuge masu amo, ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai, yabo ya tabbata ga ubangiji!” (Zabura: 150)
Zan yi shelar girmanKa, ya Allahna, Sarkina! Zan yi maKa godiya har abada abadin. Kowace rana zan yi maKa godiya, zan yabe Ka har abada abadin. Ubangiji Mai girma ne, dole ne a fifita yabonSa, girmanSa ya fi karfin ganewa. Za a yabi abin da Ka aikata daga tsara zuwa tsara, za su yi shelar manya-manyan ayyukanKa. Mutane za su yi magana a kan darajarKa da daukakarKa, ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanKa masu ban mamaki. Mutane za su yi magana a kan manya-manyan ayyukanKa, ni kuwa zan yi shelar girmanKa. Za su ba da labarin girmanKa duka, kuma su rera waka a kan alherinKa. Ubangiji Mai kauna ne, Mai jinkai, Mai jinkirin fushi, cike da madauwamiyar kauna. Shi Mai alheri ne ga kowa yana juyayin dukan abin da Ya halitta. Ya Ubangiji! TalikanKa duka za su yabe Ka, jama’arKa kuma za su yi maka godiya! Za su yi maganar darajar mulkinKa, su ba da labarin ikonKa, domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanKa da kuma darajar daukakar mulkinKa. MulkinKa, madauwamin mulki ne, Sarki ne kai har abada. Ubangiji Yakan taimaki dukan wanda yake shan wahala, yakan ta da wadanda aka wulakanta. Dukan masu rai suna sa zuciya gare Shi, Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata, Yana kuwa ba su isasshe, Yakan biya bukatarsu duka. Ubangiji Mai adalci ne a abin da Yake yi duka, Mai jinkai ne a ayyukanSa duka. Yana kusa da dukan wadanda suke kira gare Shi, wadanda suke kiranSa da zuciya daya. Yakan biya bukatar dukan wadanda suke tsoronSa, Yakan ji kukansu, Ya cece su. Yakan kiyaye dukan wadanda suke kaunarSa, amma zai hallaka mugaye duka. A kullum zan yabi Ubangiji, bari talikai duka su yabi sunanSa mai tsarki har abada.
Ka yabi Ubangiji, ya raina! Ka yabi sunanSa mai tsarki!
Ka yabi Ubangiji, ya raina! Kada ka manta da yawan alherinSa. Ya gafarta dukan zunubaina, Ya kuma warkar da dukan cututtukan. Ya cece ni daga kabari, ya sa mini albarka da kauna da jinkai. Ya cika raina da kyawawan abubuwa, don in zauna gagau, kakkarfa kamar gaggafa. Ubangiji Yakan yi wa wadanda ake zalunta shari’a ta gaskiya. Yakan ba su hakkinsu. Ya fada wa musa shirye-shiryensa. Ya yardar wa jama’ar Isra’ila su ga manyan ayyukansa. Ubangiji Mai jinkai ne, Mai kauna ne kuma, Mai jinkirin fushi ne, cike Yake da madauwamiyar kauna. Ba zai yi ta tsauta wa kullum ba, ba zai yi ta jin haushi har abada ba. Yakan yi mana rangwame sa’ar da Yake hukunta mu, ko sa’ar da Yake sāka mana saboda zunubanmu da laifuffukanmu. Kamar yadda nisan sararin sama yake bisa kan duniya, haka kuma girman kaunarSa yake ga wadanda suke tsoronSa. Kamar yadda gabas take nesa da yamma, haka nan ne Ya nisantar da zunubanmu daga gare mu. Kamar yadda uba yake yi wa ’ya’yansa alheri, haka nan kuwa Ubangiji Yake yi wa masu tsoronSa alheri. Ubangiji Ya san abin da aka yi mu da Shi, Yakan tuna da kura aka yi mu. Mutum fa, ransa kamar ciyawa ce, takan yi girma, ta yi yabanya kamar furen daji. Sa’an nan iska ta bi ta kanta, takan bace, ba mai kara ganinta. Amma kaunar Ubangiji ga wadanda suke girmama shi har abada ce. AlherinSa kuwa tabbatacce ne har dukan zamuna, ga wadanda suke rike da alkawarinSa da gaskiya, wadanda suke biyayya da umarninsa da aminci. Ubangiji Ya kafa KursiyyinSa a sama, Shi Yake sarauta duka. Ku yabi Ubangiji, ku karfafa, ku manyan mala’iku, ku da kuke biyayya ga umarninSa, kuna kasa kunne ga maganarSa! Ku yabi Ubangiji, ku dukan ikokin da suke a sama, ku yabi Ubangiji, ku bayinSa masu aikata abin da yake so! Ku yabi Ubangiji, dukanku da kuke halittattunSa, a duk inda Yake mulki! Ka yabi Ubangiji, ya raina!
(Zabura 103, 145 da 150).