✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya zama zakara bayan ya yi tafiyar kilomita 48 da kwallo a digirgire

Wani dan Najeriya mai suna Harrison Chinedu da ke kwallo a kasar Kambodiya (Cambodia) ya kafa sabon tarihi a wata gasa da aka shirya a…

Wani dan Najeriya mai suna Harrison Chinedu da ke kwallo a kasar Kambodiya (Cambodia) ya kafa sabon tarihi a wata gasa da aka shirya a Legas ta yin digirgire da kwallo.
An ce gasar ta gudana ne a ranar Lahadin da ta gabata a filin wasa na Surulere da ke Legas.
Yanzu dan kwallon ya kafa sabon tarihi bayan ya yi tafiya ta kimanin kilomita 48 yana tafiya da kwallo a digirgire a kansa ba tare da ta fadi ba.
Wannan ta sa ya shiga kundin tarihin masu yin digirgire da kwallo na duniya  (Guiness Book of Record) inda ya doke tarihin da wani sojan Indiya Naib Singh ya kafa bayan ya yi tafiya da kwallo a digirgire har na tsawon kilomita 45.64 a gasar da ta gudana a Indiya a shekarar 2011.  Sannan Naib ne ya doke tarihin da wani dan Bangaladesh mai suna Abdul Halim ya kafa tun da farko a gasar yin digirgiren da ta gudana a filin wasa na Bangahandhu da ke Dhaka a ranar 22 ga Oktoba 2011, bayan ya yi tafiya da kwallo a digirgire har na tsawon kilomita 15.2.
Cibiyar shirya gasar wasan yin digirgire da kwallo ta Dokta Rafiu Oladipo ce ta dauki nauyin shirya gasar  inda tuni ta mika kyautar zama zakara ga Harrison, sannan ta sanar da duniya shi ne sabon gwarzon masu yin digirgire da kwallo na duniya.
A lokacin da aka yi hira da shi a kan irin kalubalen da ya fuskanta a yayin gasar, Harrison Chinedu ya ce babban kalubalen da ya fuskanta ita ce yadda jijiyoyin cinyarsa suka nemi kagewa  a yayin gasar amma da taimakon Allah ya kammala ba tare da ya samu matsala ba.
Dokta Rafiu Oladipo wanda har ila yau shi ne shugaban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, cibiyarsa tana shirya irin wannan gasa ce a duk shekara.  Kuma ya ce suna yin haka ne don zakulo hazikan ’yan Najeriya ta irin wannan gasa don duniya ta san da zamansu.  Ya ce cibiyarsa tana yin haka ne don bunkasa harkokin wasanni a Jihar Legas da kuma a Najeriya baki daya.