Gobe Asabar ake shirin doka wasan karshe na Gasar Kofin Zakarun Turai tsakanin Inter Milan da Manchester City.
Da misalin karfe 8:00 na dare a agogon Najeriya za a yi karon battar a Filin Wasa na Ataturk Olympic mai daukar ’yan kallo 74,753 da ke birnin Istanbul na Kasar Turkiyya.
- Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a Aso Rock
- Liverpool ta kulla yarjejeniyar shekara 5 da Mac Allister
City dai ita ce kungiyar da ke neman kafa tarihin lashe babbar gasar ta Turai a karon farko yayin da Inter Milan ke fatan ganin ta lashe kofin cikon na hudu a tarihi.
Tun a shekarar 2008 ne lokacin da City ta koma hannun Larabawan Abu Dhabi, yau shekaru 15 kenan kungiyar da ke Manchester ta fara fafutukar ganin ta cimma nasarar lashe kofin gasar Zakarun na Turai.
Masu fashin baki da dama sun fi kyautata zaton cewa City ce za ta samu nasara a wasan na gobe da za ta fafata ta Inter Milan.
Daga cikin dalilin masu sharhin kuwa akwai ganin yadda kungiyar ba ta yi rashin nasara ko da sau guda ba a gasar zakarun Turai ta bana, yayin da kuma bayan shiga zagayen ‘yan sha shida, da kwata final da kuma daf da na karshe, kungiyar ta zazzaga wa abokan hamayyar da ta kara da su wato RB Leipzig, da Bayern Munich da kuma Real Madrid kwallaye a raga.
A bana ma dai Manchester City ce ta sake lashe kofin Firimiyar Ingila a karo na uku a jere yayin da Arsenal ta gaza katabus bayan shafe watanni tana jan ragamar teburin gasar.
A bangaren Inter Milan kuwa, sau uku kungiyar ta taba lashe kofin Gasar Zakarun Turai, sai dai rabon ta da kofin, tun shekarar 2010, lokacin da kulob din ke karkashin Jose Mourinho.